Garba Shehu yace Manoman da aka kashe ba su samu izinin shiga gona ba

Garba Shehu yace Manoman da aka kashe ba su samu izinin shiga gona ba

- Garba Shehu ya yi karin haske game da harin da aka kai a Garin Zabarmari

- Hadimin Shugaban kasar ya daura laifin a kan mutanen da su ka koma gari

- A cewarsa, sai sojoji sun ba al'umma umarni kafin su tare a wasu yankunan

Fadar shugaban kasa ta sake yin magana a game da kisan gillar da aka yi wa wasu Bayin Allah a karshen makon nan a garin Zabarmari, jihar Borno.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa manoman da aka kashe sun shiga gona ne ba da izinin hukuma ba.

Garba Shehu ya daura laifi a kan wadannan Bayin Allah da suka riga mu gidan gaskiya, ya ce sojoji ba su amince masu zuwa cikin gonakinsu ba.

KU KARANTA: Harin Zabarmari: Mun gaji da gafara sa, babu abin da za a iya – CNG

An hallaka manoman ne a gonakin shinkafarsu, fadar shugaban kasa tana ganin akwai sakacinsu.

Malam Garba Shehu ya bayyana haka ne a lokacin da manema labarai su kayi hira da shi a gidan jaridar BBC, a ranar Litinin 30 ga watan Nuwamba, 2020.

Da aka tambayi babban hadimin shugaban kasar ko ya na zargin mutanen da laifi ne, sai ya bayyana cewa gaskiya ce ta kama, kuma dole a fade ta duk dacinta.

"Ba haka ba ne, gaskiya ce da sai an fade ta."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yanka wuyan Malamin Makaranta a FUAM

Garba Shehu yace Manoman da aka kashe ba su samu izinin shiga gona ba
Garba Shehu Hoto: Pulse.ng
Asali: Twitter

“Gwamnati tana takaicin wannan lamari. Manoma da ba su ji ba-ba su gani ba 43 ko kimanin haka, ‘yan ta’adda marasa tausayi suka yanke masu makwogoro.”

“Ya kamata mutane su san halin da ake ciki a yankin tafkin Chadi.” Inji Malam Garba Shehu.

Hadimin ya ce: “Saboda haka ya kamata a irin wadannan yankuna, sai an samu na’am daga jami’an tsaro kafin manoma ko ‘yan gari su koma aiki a kasarsu.”

Ya ke cewa: “Sun samu izini daga jami’an tsaro da ke rike da wurare? An fada wa wasu su koma aiki. An fada mani jami’an tsaro ba su ce a koma ba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel