Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu

Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu

- Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana dalilin da yasa Shugaba Buhari ke ci gaba da ajiye shugabannin tsaro

- Shehu ya ce nada shugabannin tsaro ko tsige su ikon shugaba ne, kuma yana da damar ci gaba da barinsu idan har ya gamsu da kokarinsu

- Ya ce sam kiraye-kirayen da ake yi na sauke su baya bisa hanya

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya ce kiraye-kiraye da ake yi na a sallami shugabannin tsaro baya kan layi.

A cewar Shehu, Shugaban kasar na da ikon nadawa ko sallamar shugabannin tsaro, inda ya kara da cewa Shugaban kasar na ajiye shugabannin tsaro idan har ya gamsu da kokarinsu.

Legit.ng ta rahoto batun harin da aka kai jihar Borno inda aka kashe akalla manoman shinkafa 43 a garin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a ranar Asabar da ta gabata.

Boko Haram: Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu
Boko Haram: Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Wannan lamari ya sabonta kiraye-kirayen da al’umman kasar ke yi na neman gwamnatin tarayya ta tsige shugabannin tsaro sannan ta maye gurbinsu da wasu sabbi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Borno ya lissafa wasu muhimman abubuwa 7 da ya kamata Buhari yayi don kawo karshen Boko Haram

Da yake martani ga kiraye-kirayen yan Najeriya wadanda ke so a sauya fasalin tsaron kasar, Shehu ya ce shawarar sallama ko ci gaba da barin kowani shugaban tsaro ya rataya ne a kan wuyan Shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Kakakin Shugaban kasar ya ce: “Ban san da cewa akwai wata takamaiman doka da ta yi magana a kan wa’adin shugabannin tsaro ba. Suna aiki ne bisa ra’ayin Shugaban kasa sannan idan har Shugaban kasar ya gamsu da kokarinsu, sai ya barsu su ci gaba. Lamarin na kan teburinsa ne-tare da mutunta ra’ayin yan Najeriya.

“Kira ga tsige shugabannin tsaro baya kan layi duba ga cewar Shugaban kasar ba dan abi yarima a sha idan jam’iyyar adawa wacce ke ta wannan kira bane a duk lokaci. Gaba daya wannan shawararsa; shi ke yanke hukunci kan wanda zai bari a matsayin shugabannin tsaro kuma na tsawon wani lokaci.”

An tattaro cewa mayakan Boko Haram sun fara daure manoman, wadanda ke aiki a gonar shinkafa, kafin suka yi masu yankan rago.

Shehu ya ce manoman basu nemi izinin sojoji ba na aiki a gonakin shinkafar lokacin da harin ya afku.

Martaninsa ya haifar da cece-kuce a kan shafukan zumunta yayinda yan Najeriya suka caccake shi kan ganin laifin matattun da yayi.

KU KARANTA KUMA: Mijina mafadaci ne, rannan ya murde mani wuya har sai da na suma, mata ga kotu

A gefe guda, Dr. Ahmad Lawan ya gabatar da wata mafita ga gwamnatin tarayya don magance lamarin Boko Haram.

Shugaban majalisar dattawan da yake rokon gwamnati ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ya dace a sauya fasalin tsaron kasar.

Lawan ya yi kiran ne a lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa zuwa jihar Borno kan mummunan kisan kiyashi da aka yi wa manoman shinkafa 43.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel