Rubdugun martani: Garba Shehu ya yi laushi, ya ce ba'a fahimci kalamansa da kyau ba a kan kisan manoma

Rubdugun martani: Garba Shehu ya yi laushi, ya ce ba'a fahimci kalamansa da kyau ba a kan kisan manoma

- Har yanzu batun kisan manoma 43 a Zabarmari da ke jihar Borno ya na cigaba da daukar hankali

- A wata tattauna da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce har yanzu akwai wuraren da sai an shawarci sojoji kafin a ziyarcesu

- A cewarsa, yankin gonakin Zabarmari na daga cikin wuraren da jami'an tsaro suka ware a matsayin masu hatsarin gaske

Jama'a sun fusata da jin kalaman Garba Shehu a kan cewa manoman da aka kashe a jihar Borno sun koma gonakinsu ba tare da izinin rundunar soji ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a kan halin da tsaro ke ciki a jihar Borno bayan 'yan Boko Haram sun kashe manoman a ranar Asabar.

Da ya ke karin haske a kan fahimtarsa ba daidai ba da jama'a suka yi, Garba Shehu ya ce an yi masa mummunar fassara.

"A yau na tsinci kaina a matsayin abin tattaunawa a dandalin sada zumunta saboda mummunar fahimtar da aka yi wa kalamaina.

KARANTA: Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid

"Ita dai jihar Borno da ake magana a kanta, a hannun sojoji take har yanzu, duk wani abu ko wata mu'amala da jama'a za su yi suna karkashin tsaro.

Rubdugun martani: Garba Shehu ya yi laushi, ya ce ba'a fahimci kalamansa da kyau ba a kan kisan manoma
Rubdugun martani: Garba Shehu ya yi laushi, ya ce ba'a fahimci kalamansa da kyau ba a kan kisan manoma @Channels
Asali: Twitter

"Kungiyoyi ma su zaman kansu da 'yan kasuwa da sauransu su kan nemi shawara daga rundunar soji domin zuwa wasu yankuna masu hatsari a jihar Borno.

"Hukumomin tsaro sun saka yankin gonakin kauyen Zabarmari a cikin yankuna masu hatsari, a saboda haka sai an yi shawara da su kafin ziyartar wurin.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

"Babu wanda ya ke farin ciki da kisan kare dangi da aka yi wa manoma a Zabarmari, babu kuma wanda zai karu da wani abu idan ya saka wasa a cikin lamarin.

"Tambayar da na yi kokarin amsawa a BBC ita ce: ko jami'an tsaro sun cire yankin daga cikin masu hatsari, wanda za'a iya ziyarta ba tare da shawartarsu ba? maganar gaskiya shine, a'a," kamar yadda Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na tuwita.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, an dawo da wani tsohon bidiyo da shugaba Buhari ke zargin gwamnatin tarayya da zama babbar mai daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke takara, gabanin zaben shekarar 2015.

Dawo da bidiyon tamkar tuni ne ga shugaba Buhari domin ya tuna alakwuran da ya daukarwa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel