Yemi Osinbajo: Gwamnoni sun amince da manufar NMFPAN na 2021-25

Yemi Osinbajo: Gwamnoni sun amince da manufar NMFPAN na 2021-25

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya fito da tsarin NMFPAN

- Idan aka yi amfani da tsarin nan, ana sa rai yunwa za ta ragu a Najeriya

- Gwamnatin Tarayya za ta dabbaka wannan manufa tsakanin 2021-2025

Majalisar kula da cin abinci mai lafiya a Najeriya ta amince da wani tsari na shekara biyar da aka fito da shi domin maganin yunwa a kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana sa ran manufa da gwamnati ta zo da shi zai taimaka wajen yaki da matsalar samun abinci mai lafiya.

Mai girma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda ya ke jagorantar wannan majalisa, ya amince da tsarin NMFPAN na 2021-2025.

Manufar National Multi-Sectoral Plan of Action for Food and Nutrition zai yaki karancin abinci mai lafiya da gina jiki daga shekara mai zuwa.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta ratsa gidan Sojojin kasa, 26 sun kamu

Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman da wannan majalisa ta yi jiya ne ta kafar yanar gizo.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, idan aka yi amfani da wannan tsari, akalla 50% na masu fama da matsalar karancin abinci mai kyau za su ragu.

Bayan haka za a samu karuwar mata masu baikon nono tsan-tsa zuwa 65%, yara ‘yan kasa da shekara biyar masu fama da yunwa za su ragu.

Mataimakin shugaban kasar ya nuna a shirya yake ya karbi duk wasu shawarwari daga sauran masu ruwa da tsaki da kuma jami’an gwamnati.

KU KARANTA: Sanata Dino Melaye ya fara da-na-sani, ya nemi afuwar Jonathan

Yemi Osinbajo: Gwamnoni sun amince da manufar NMFPAN na 2021-25
Yemi Osinbajo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya yi na’am da wannan manufofi a madadin sauran gwamnoni.

Dazu kun ji cewa wasu manyan magoya bayan jagoran jam'iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu, sun kaddamar da yakin neman zabensa.

Magoya bayan 'dan siyasar sun hada da wasu tsofaffin Ministoci, yan majalisa da jiga-jigan 'yan siyasa wanda su ke ganin Bola Tinubu zai ci a 2023.

'Yan kwamitin yakin neman zaben sun yi kira ga jama'a su goyi bayan Tinubu a zabe mai zuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel