Janar Sagir Musa ya ce Jami’ai 26 sun kamu, sojoji sun killace kansu bayan taro

Janar Sagir Musa ya ce Jami’ai 26 sun kamu, sojoji sun killace kansu bayan taro

- Gwajin da aka yi ya nuna cewa manyan sojoji 26 suna da Coronavirus

- Janar Sagir Musa ya ce an yi wa Jami’ai fiye da 400 gwaji zuwa yanzu

- An fara gwajin a gidan soja ne bayan Janar John Irefin ya kamu da cutar

Akalla Janarori da manyan sojoji 26 aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar nan ta COVID-19, inji gidan sojin kasan Najeriya.

Rundunar sojan kasan Najeriya ta ce an yi wa sojoji 417 gwajin cutar Coronavirus bayan cutar ta kashe shugaban runduna ta 6, John Irefin.

Ana zargin cewa COVID-19 ce ta hallaka Manjo Janar John Irefin a makon da ya gabata a Abuja.

Jami’in hulda da jama’a da yada labarai, Birgediya Janar Sagir Musa ya fitar da jawabi a ranar Litinin, ya bayyana wannan labari maras dadi.

KU KARANTA: Boko Haram sun hallaka mutanen Borno da ke kasar Nijar

Sagir Musa ya ce ana yi wa duka jami’an da ke aiki a Hedikwatar sojojin kasa gwaji, sannan ana cigaba da bin dokokin takaita yaduwar COVID-19.

Kamar yadda Birgediya Janar Sagir Musa ya bayyana a jawabin na sa, cutar ta sake barkowa jami’an tsaron ne wajen babban taron sojojin kasa.

“Bayan an tabbatar da cewa John Irefin ya kamu da COVID-19 a ranar 9 ga watan Disamba, 2020, COAS ya bada umarni duk wadanda su ka halarci taron su yi maza su killace kansu.”

Jawabin ya ce: “Bayan haka, an fara gudanar da cikakken gwaji ga duka wadanda suka halarci taron.”

KU KARANTA: Mun tsefe Sambisa lokacin ina Soja - Sultan ya bukaci a cika daji

Janar Sagir Musa ya ce Jami’ai 26 sun kamu, sojoji sun killace kansu bayan taro
COAS, Janar Tukur Buratai Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Zuwa ranar 13 ga watan Disamba, 2020, an yi wa jami’ai 417 gwaji, an samu 26 da suke dauke da cutar." Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto dazu.

A farkon makon nan ne mu ka samu samu labari cewa gwamnatin Amurka ta soma aika sabon maganin COVID-19 da aka kirkiro kwanan nan zuwa kasashe.

Hukumomin sun yarda a fara aiki da wannan sabon magani na PFizer da ake sa ran cewa zai kawo karshen Coronavirus da ta addabi kasashen Duniya.

Rahotanni sun ce za ba Mutanen Amurka miliyan 100 maganin domin rigakafi daga COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel