Dino ya roki Jonathan: Kayi hakuri abin da nayi maka a baya, ido na ne ya rufe
- Dino Melaye ya fito ya na yabon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
- Tsohon Sanatan na Kogi yace idonsu ya rufe ne lokacin da su ka rika adawa
- Melaye yace kiran Buhari da Jonathan ya yi a waya ya taimaki kasar a 2015
A ranar Talata, 15 ga watan Disamba, 2020, tsohon Sanatan Najeriya, Dino Melaye, ya nemi afuwar Dr. Goodluck Jonathan a gaban Duniya.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Sanata Dino Melaye ya nemi tsohon shugaban kasar ya yafe masa abubuwan da ya faru tsakaninsu a baya.
Tsohon ‘dan majalisar ya bayyana wannan ne a wajen kaddamar da wani littafi da aka yi game da rawar da ya taka wajen rusa PDP a zaben 2015.
Ya ce: “Ni Sanata Dino Melaye, ina so in fada a fili cewa bayan abubuwan da suka faru sun faru daga baya, ina so in fada a gaban Duniya cewa da idanu na sun makance, yanzu ina gani.”
KU KARANTA: Dino ya na tika rawa
‘Dan siyasar ya cigaba: “A shekarar 2017, an kama ni sau 18, an yi fiye da wannan a 2018, kuma a tsakanin wancan lokaci zuwa yanzu, an kai ni kotu sau 12.”
Melaye ya ce kara daya ya rasa, wanda aka zarge shi da laifin yunkurin hallaka kansa da kansa.
“Ina mamakin mutum irina mai son Duniya da kaunar motoci zai nemi ya kashe kansa.” Inji Dino.
“Ya shugaba Jonathan, a madadin sauran wadanda idanunmu su ka rufe, ina so in ce, ka yi hakuri... Abin da na ke mamaki shi ne wayar da ka kira.”
KU KARANTA: Kudin makamai: Sambo Dasuki zai san matsayarsa a Kotu
Ganin abin da yake faruwa a Amurka, Dino Melaye ya ce da Jonathan bai kira Buhari a 2015 lokacin da ya fadi zabe ba, da wani labarin ake yi yanzu.
“Ina mamaki wani lokaci, in ce da ba ka yi wayar nan ba, da ba ya inda ya ke a yau. Kadan ne irinka.” Dino ya fada ya na mai neman albarkar Dr. Jonathan.
A baya kun ji cewa Dino Melaye ya hadu da tsohon shugaba Goodluck Jonathan. Hakan ta faru ne a lokacin da ake rade-radin fitowarsa takarar shugaban kasa a 2023.
Tsohon dan majalisa, Dino Melaye, ya wallafa hoton wannan haduwar ta su a shafinsa na Twitter.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng