Masu tada kafar baya sun kashe mutanen Najeriya 50 da su ka fake a Tumuk
-Ana zargin Sojojin Boko Haram sun shiga har Jamhuriyyar Nijar, sun yi ta’adi
-A wani hari da aka kai a ranar Asabar, an hallaka mutanen Najeriya a Tumuk
-Akwai mutanen jihar Borno da dama da su kayi gudun hijira, suka fake a Nijar
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2020, game da wani mummunan hari da ‘Yan ta’adda suka kai a makwabta.
Ana zargin cewa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a garin Tumuk, da ke kasar Jamhuriyyar Nijar, an kai harin ne a karshen makon jiya.
A sanadiyyar wannan hari ne aka hallaka mutanen Najeriya akalla 50 da su ke gudun hijira a Tumuk.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’ddan sun budawa Bayin Allah wuta ne bayan sun rutsa su daf-da-daf, sannan kuma suka rusa wasu gidajensu.
KU KARANTA: Miyagu sun kashe wani Manomi, sun sace mata 2 a Jihar Katsina
Mafi yawan wadanda aka kashe a wannan hari na ranar Asabar, mutanen garin Abadam ne daga jihar Borno, wadanda su ka samu mafaka a kasar ta Nijar.
Akwai mutanen karamar hukumar Abadam a jihar Borno da su ka tsero daga Najeriya zuwa Jamhuriyyar Nijar bayan harin Boko Haram ya yi kamari.
Jaridar ta bayyana cewa akwai mutanen Najeriya sama da 40, 000 da su ke gudun hijira a Tumuk.
A farkon shekarar nan ne wasu daga cikin wadanda su ka yi gudun hijira daga Abadam su ka dawo gida babu girma da arziki, a sakamakon irin wannan hari.
KU KARANTA: Ƴan ta'adda sun kai hari a kasuwa, sun kashe rai
Kawo yanzu ‘yan ta’addan Boko Haram ba su fito sun yi magana, sun tabbatar da cewa su ne su ka kai wannan hari na Tumuk, kamar yadda su ka saba yi ba.
A jiya kun ji yadda ga baki ga hanci, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki zuwa Kankara daga Daura domin yi wa jama'a jajen satar 'ya 'yansu.
Kamar yadda kuka sani shugaban kasar ya aika tawaga ne tun daga Abuja zuwa Kankara, ya yi zamansa a gidansa da ke garin Daura da ke cikin jihar Katsina.
A maimakon shugaban kasar ya kai ziyara da kansa, sai ya aika wakilai daga birnin tarayya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng