GSSS Kankara: Mun gano wasu Dalibai 17 da aka sace inji Gwamnan Jihar Katsina

GSSS Kankara: Mun gano wasu Dalibai 17 da aka sace inji Gwamnan Jihar Katsina

- Gwamnan Katsina yace wasu ‘Yan makarantar da aka sace a Kankara sun kubuta

- Hon. Aminu Bello Masari ya tsaida adadin Daliban da su ka tsira kawo yanzu a 17

- Gwamnan ya sha alwashin ceto ragowar yaran da ake zargin suna dajin Zamfara

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bayyana cewa an gano wasu daga cikin daliban makarantar Kankara da aka sace a ranar Juma’a.

Mai girma gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da gidan rediyon Deutsche Welle ya yi hira da shi a ranar Litinin, 15 ga watan Disamba, 2020.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari yace wasu cikin yaran makarantar sun tsira daga hannun ‘yan bindiga, kawo yanzu sun koma cikin 'yanuwansu.

Gwamnan ya ce mafi yawan yaran makarantar GSSS Kankara da aka yi gaba da su, su na tsare a cikin wani kungurmin daji a yankin jihar Zamfara.

KU KARANTA: An yi ca a kan Shugaba Buhari na gaza zuwa duba mutanen Kankara

Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa suna kokarin kubutar da wadannan ‘yan makaranta da ke hannun ‘yan ta’addan da su ka rabasu da gidajensu.

“A yau (Litinin), bayanan da suke kara zuwa mani sun nuna an gano 17 daga cikin yaran da aka sace. An gano 15 daga cikinsu ne a Dinya a Danmusa.”

Ya ce: “DPO ya fada mani wannan. An kuma gano wani guda daga cikinsu, mahaifin na karshe kuma ya kira, ya bayyana cewa yaronsa ya dawo gida.”

“Duka wadannan yara da aka gano, sun koma wajen ‘yanuwansu, tun da mun rufe makarantu.”

KU KARANTA: Mu ne mu ka sace 'Yan makarantar kwana - Boko Haram

GSSS Kankara: Mun gano wasu Dalibai 17 da aka sace inji Gwamnan Jihar Katsina
Shugaban kasa da Gwamnan Jihar Katsina Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: Twitter

Game da maganar da ake yi da ‘yan bindigan, Masari yace sun kira wani malami (da aka sace ‘dansa) sun fada masa jirgin sama ya daina masu shawagi.

Gwamnan yace yawancin yaran suna dajin Zamfara. “Muna kokarin ceto su nan da kwanaki biyu zuwa uku. Muna baran addu’a, da neman hakurin iyaye.”

A jiya kun ji cewa an gano yawan ‘Yan makarantar na GSSS Kankara da miyagu su ka sace. An gano adadin ne bayan wani Dalibi guda ya samu ya kubuta.

Wannan yaro mai suna Osama Aminu Maale da ya samu ya tsere yace su 520 aka sace. Alkaluman na sa ya sha banbam da na hukumomin gwamnati.

Osama Aminu Maale yace rashin lafiya ta cece sa, aka yi masa nisa, shi kuma ya samu ya tsere.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel