Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka zuwa APC

Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka zuwa APC

- Jam'iyyar APC mai mulki ta samu karuwa na wasu mabobin majalisar wakilai biyu

- Yan majalisar biyu daga jihohin Kano da Taraba sun baro tsoffin jam'iyyarsu saboda rikicin shugabanci

- Datti Yako ya bar jam'iyyarsa ta PDP yayinda Danjuma Usman Shiddi ya sauya sheka daga APGA

Wasu mambobin majalisar wakilai guda biyu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yau Talata, 15 ga watan Disamba.

Yan majalisar sun sanar da shawarar da suka yanke a cikin wasu wasiku mabanbanta wanda kakakin majalisar ya karanto a zauren majalisar.

Yan majalisar sune Datti Yako daga jihar Kano da kuma Danjuma Usman Shiddi daga jihar Taraba, kuma dukkaninsu sun daura alhakin sauya shekarsu kan rikicin shugabanci da ake fama dashi a jam’iyyunsu.

Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka zuwa APC
Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka zuwa APC Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria

Mista Yako ya sauya sheka ne daga babbar jam’iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP), inda shi kuma Mista Shiddi ya baro jam’iyyarsa ta All Progressive Grand Alliance (APGA).

Jam’iyyar APC ta wallafa batun sauya shekar yan majalisar a shafinta na Twitter yayinda take masu maraba da dawowa cikinta.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

A wani labarin kuma, Sanatoci hudu da aka zaba a zaben cike gibin da hukumar INEC ta gudanar kwanaki goma da suka gabata sun samu shiga zauren majalisa ranar Talata, 15 ga Disamba.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya rantsar da su. Magatakardan majalisan ya gabatar musu da rantsuwar a matsayin sabbin sanatoci.

Ana kyautata zaton za su wakilci al'ummarsu ta hanyar gabatar da kudirai masu amfani don cigaban kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel