Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita

Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita

- Jirgin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya daga zuwa kasar Amurka a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba

- A cikin wasikar da ya aike majalisar dokokin jihar, Sule ya bayyana cewa zai je ganin likita ne na tsawon wasu kwanaki

- Ya kuma mika ragamar mulkin jihar a hannun mataimakinsa har zuwa lokacin da zai dawo

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya tafi kasar Amurka domin duba lafiyarsa a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A bisa wasikar sanar da batun tafiyar wanda Gwamna Sule ya aike wa majalisar dokokin jihar Nasarawa, ya bayyana cewa zai dawo kasar a ranar 29 ga watan Disamba.

Ya kuma bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar, Dr Emmanuel Akabe, zai ci gaba da kula da duk wasu lamura da suka shafi jihar zuwa lokacin da zai dawo.

Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu

Kakakin majalisar dokokin jihar, Ibrahim Balarabe Abdullahi, shine ya bayyana hakan yayinda yake karanto wasikar gwamnan a zauren majalisar mai taken, ‘sanar da batun tafiyana kasar Amurka.'

Wasikar ya zo kamar haka:

“Ina fatan sanar da mai girma kakakin majalisa cewa zan yi tafiya zuwa kasar Amurka domin duba lafiyana daga ranar Lahadi, 13 ga wata zuwa ranar Asabar, 29 ga watan Disamba, 2020.

“Kuma, a bayan idona, mataimakin gwamna, Dr Emmanuel Akabe zai jagoranci duk wasu harkoki na jihar har zuwa lokacin da zan dawo.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdulaziz Gafasa, da wasu sauran shugabanni biyu sun yi murabus daga mukamansu.

Gafasa ya sanar da yin murabus dinsa ne a cikin wata wasika da ya mikawa magatakardar majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Harin Kankara: Har yanzu dalibai 10 ne a hannun masu garkuwa da mutane koda dai ba a tabbatar ba, In ji Garba Shehu

Wata majiya daga majalisar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta sanar da Premium Times da safiyar ranar Talata, cewa Gafasa tare da wasu shugabannin majalisar biyu sun yi murabus daga mukamansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel