Pele, Ronaldo, Messi, da Cristiano su na cikin sahun farkon XI na Taurarin ‘Yan kwallo
- ‘Yan jarida 140 sun fitar da jerin gwarazon ‘Yan wasan da aka yi a Duniya
- Wadannan sune ‘Yan wasan kwallon kafan da ake ganin sam ba su da sa’o’i
- Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun shiga jerin, Zinedine Zidane bai ciki
An fito da jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ba a taba yin irinsu ba. France Football ce tayi wannan aiki da taimakon wasu kwararrun ‘yan jarida 140.
Jaridar The Sun ta ce an zabi rukunin ‘yan wasa 11 har kashi uku. Irinsu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suna cikin sahun farko na jerin taurarin.
Rahoton ya tabbatar da cewa tsofaffin ‘yan wasa Pele da marigayi Diego Maradona sun samu shiga wannan sahu, amma babu wurin Zinedine Zidane.
‘Dan wasan da aka sa a ragar wannan tawaga shi ne Marigayi Lev Yashin na tsohuwar kasar Rasha.
KU KARANTA: Abin da ya sa ba za a manta da Maradona ba
An zabi ‘yan wasan baya uku a jerin, an yi amfani ne da salon 3-4-3. ‘Yan bayan da aka sa su ne: Cafu, Franz Beckenbauer da kuma Paolo Maldini.
Wadanda su ke cikin ‘yan wasan tsakiya su ne: Diego Maradona da Pele a gefe, sai kuma Lothar Matthaus da Xavi, wanda su ne ‘yan shekarun nan.
A sama akwai Ronaldo da takwaransa Cristiano Ronaldo da kuma sa’ansa, Lionel Messi. Dukkaninsu, ‘yan kwallon da aka yi a zamanin nan ne.
Sahu na biyu da aka yi ya kunshi: Gianluigi Buffon, Carlos Alberto, Franco Baresi, Roberto Carlos, Zinedine Zidane, Andrea Pirlo, Frank Rijkaard, Alfredo Di Stefano, Garrincha, Johan Cruyff da Ronaldinho.
KU KARANTA: ‘Yan wasan da suka tsiyace bayan sun yi ritaya
Ragowar tawagar ita ce ta Manuel Neuer, Philipp Lahm, Sergio Ramos, Paul, Michel Platini, Johan Neeskens, Didi, Andres Iniesta, George Best, Marco van Basten, da Thierry Henry.
Kwanakin baya labari ya zagaye ko ina na mutuwar tsohon 'dan kwallon kasar Argentina Diego Maradona, wanda ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Maradona ya dade yana fama da matsalar hunhu da ciwon kwakwalwa. Dama tun bayan da ya yi ban-kwana daga kwallon kafa, Maradona ya yi ta fama da ciwo.
Ana zargin cewa rashin lafiya da kuma karin kibar marigayin ta na da nasaba da shan kwayoyi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng