Lokutan da tsohon Tauraron kwallon kafa Maradona ya yi suna a tarihi

Lokutan da tsohon Tauraron kwallon kafa Maradona ya yi suna a tarihi

- Tsohon ‘Dan wasan Duniya, Diego Maradona ya mutu yana shekara 60

- Mun kawo abubuwan da za a rika tuna Diego Maradona da su har gobe

- Daga ciki har da nasarorin da ya samu a gida da Napoli a 1986 da 1987

A ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2020, aka samu labarin cewa tsohon ‘dan wasan Duniya, Diego Armando Maradona ya mutu, yana mai shekaru 60.

Jaridar Vanguard ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da Marigayin ya yi, wanda za su sa ko bayan mutuwar ta sa a cigaba da tuna wa da shi a Duniya.

1. Gwarzo a gasar 1979

Kocin Argentina, Carlos Menotti bai dauki Diego Maradona zuwa gasar kofin Duniya a 1978 ba. A 1979 da aka yi gasar Jafan, Maradona ya nuna kwarewarsa har ya zama ‘dan wasan gasar.

KU KARANTA: Tsohon 'Dan kwallo, Kocin Aregina Maradona ya cika

Kusan tun daga nan ba Argentina ba ta sake kuskuren rashin gayyatar Diego Maradona wasa ba.

2. Kofin Duniya (1986)

A gasar cin kofin Duniya na 1986 ne Diego Maradona ya ci shahararriyar kwallonsa da hannu. A wannan wasa ne kuma Maradona ya yanke ‘yan wasan Ingila rututu, ya zura kwallo a raga.

3. Nasarori da Napoli a 1987

Bayan ya taya Argentina cin kofin Duniya, Diego Maradona ya kai kungiyar Napoli ga nasara bayan a da ba ta tabuka abin kirki. A dalilinsa ne ta ci gasar Seria A da Coppa Italia a 1987.

KU KARANTA: 'Dan wasan Najeriya ya mutu ana tsakiyar buga kwallo

Lokutan da tsohon Tauraron kwallon kafa Maradona ya yi suna a tarihi
Diego Maradona Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

4. Gasar kofin Duniya (1994)

A gasar 1994, Diego Maradona ya gamu da abin kunya a Amurka, inda aka hana shi buga wasa bayan da aka zarge shi da laifin shan miyagun kwayoyi, wannan abin ya kunyata Argentina.

5. Gayyatar fushin Najeriya a 2018

Maradona ya sake bata wa Super Eagles da Najeriya rai a gasar 2018, inda ya nuna ‘yan yatsunsa bayan Marcos Rojo ya zura wa Argentina kwallo ana daf da tashi a filin wasan Krestovsky.

A baya kun ji labarin cewa tsohon Tauraron Super Eagles, Christian Obodo, ya sake shiga hannun Miyagu. Tsohon 'Dan kwallon ya fara tunanin barin gari saboda matsalar rashin tsaro.

A 2012, an taba yin garkuwa da Obodo, ana zargin har sai da aka biya wasu kudi sannan ya fito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng