Diego Maradona ya mutu yana da shekaru 60 a duniya
- A baya bayan nan ne aka sallamo Diego Maradona daga asibiti bayan yi masa tiyatan kwakwalwa
- An gano cewa akwai gudan jini a kwakwalwarsa hakan yasa aka yi masa tiyatan gaggawa
- Fitaccen dan wasan ya rasu a ranar Laraba 25 ga watan Nuwamban shekarar 2020
Shahararren dan kwallo duniya dan kasar Argentina, Diego Maradona ya rasu. Ya rasu ne a gidansa da ke Tigre bayan bugun zuciya a cewar rahotanni daga kasar Argentina.
Fitaccen dan kwallon wanda ya yi mafi yawancin wasanninsa a Napoli ya kuma buga wa kungiyar Barcelona wasa. Ya rasu a babban birnin Argentina Buenos Aires inda nan ne dama garinsu.
Maradona ya rasu yana da shekaru 60 a duniya kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Tun bayan yin murabus dinsa daga kwallon kafa, shaharren dan wasan ya yi ta fama da rashin lafiya da kuma kara kiba wadda ke da nasaba da shan kwayoyi da ya fara tun lokacin yana buga kwallo.
DUBA WANNAN: Abinda dan majalisar Burtaniya ya fadi game da Gowon ba gaskiya bane, in ji Shehu Sani
Maradona ya kuma rike mukamin kyaftin a kungiyar kwallon kafa na Argentina inda suka kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya na 1990 amma suka sha kaye a hannun kasar Jamus.
A kasarsa, ya lashe kofin Serie A guda biyu a lokacin da ya ke buga wa Napoli wasa da kuma kofin league a 1987 da kofin UEFA guda daya.
Ya kuma buga wasa na kankanin lokaci a kungiyar Barcelona inda ya lashe kofi guda uku a 1983 kafin daga baya su samu rashin jituwa da mahukunta kungiyar.
A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng