Jerin sabbin Sanatocin da aka rantsar yau a majalisar dattawa

Jerin sabbin Sanatocin da aka rantsar yau a majalisar dattawa

- Wani sabon rahoto ya nuna cewa an cike gurbin dake majalisar dattawan tarayya

- An yi bikin rantsar da sabbin Sanatoci a ranar Talata, 15 ga Disamba 2020

- Shugaban majalisar dattawa da magatakardan majalisan suka jagoranci bikin

Sanatoci hudu da aka zaba a zaben cike gibin da hukumar INEC ta gudanar kwanaki goma da suka gabata sun samu shiga zauren majalisa ranar Talata, 15 ga Disamba.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya rantsar da su.

Magatakardan majalisan ya gabatar musu da rantsuwar a matsayin sabbin sanatoci.

Ana kyautata zaton za su wakilci al'ummarsu ta hanyar gabatar da kudirai masu amfani don cigaban kasa.

Ga jerin sabbin Sanatocin:

1. Adetokunbo Abiru (Lagos ta gabas)

2. Henry Seriake Dickson (Bayelsa ta yamma)

3. Cleopas Moses (Bayelsa ta tsakiya)

4. Nora Ladi Dadu’ut (Plateau ta kudu)

KU DUBA: Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

Jerin sabbin Sanatocin da aka rantsar yau a majalisar dattawa
Jerin sabbin Sanatocin da aka rantsar yau a majalisar dattawa Credit: @NGRSenate
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

A bangare guda, wasu mambobin majalisar wakilai guda biyu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yau Talata, 15 ga watan Disamba.

Yan majalisar sun sanar da shawarar da suka yanke a cikin wasu wasiku mabanbanta wanda kakakin majalisar ya karanto a zauren majalisar.

Yan majalisar sune Datti Yako daga jihar Kano da kuma Danjuma Usman Shiddi daga jihar Taraba, kuma dukkaninsu sun daura alhakin sauya shekarsu kan rikicin shugabanci da ake fama dashi a jam’iyyunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng