Tsageru sun hana ‘Yan Coalition of Northern Group yin taro a Arewa House

Tsageru sun hana ‘Yan Coalition of Northern Group yin taro a Arewa House

-Kungiyar CNG ta shirya yin taro a game da sha’anin tsaro a Jihar Kaduna

-Wasu sun hana Coalition of Northern Group yin wannan taro a yau da safe

-Wadannan bata-gari sun je sun fatattaki mutane daga dakin Arewa House

Wasu gungun mutane da ake zaton ‘yan daba ne, sun tarwatsa wani taro da ake shirin gudanar wa a jihar Kaduna, The Sun ta fitar da wannan rahoto.

Gamayyar kungiyar Arewa, Coalition of Northern Group (CNG) ta shirya yin taro a kan harkar tsaro a Arewa House yau, amma abin bai yiwu ba.

Jaridar The Sun ta ce wadannan mutane da ake zargin tsageru ne sun shiga dakin taro na Arewa House, jihar Kaduna, suka fatattaki Bayin Allah.

‘Yan daban sun auka wurin taron ne da kimanin karfe 11:00 na safiyar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020, bayan masu halartar taron sun zauna.

KU KARANTA: Satar Yara: An yi ca a kan Buhari na gaza zuwa duba mutanen Kankara

Rahotanni sun bayyana cewa tsagerun sun yi kaca-kaca da teburan da aka shirya na zaman na yau.

Bayan haka, ‘yan daban sun karbe wayoyin jama’a da su ka zo wannan wuri da nufin sauraro ko bada gudumuwa a taron da aka shirya kan harkar tsaro.

An yi wa wannan taro na ranar Litinin da safe take da suna “Arewa Security Review”.

Shugaban kungiyar Arewan ta Coalition of Northern Group, Mista Balarabe Rufai, ya zanta da ‘yan jarida bayan wannan mummunan hari da aka kai.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun hallaka Manomi a Katsina yayin da Buhari ya ke Daura

Sufetan 'Yan Sanda na kasa
Sufetan 'Yan Sanda na kasa Hoto: nairametrics.com
Source: UGC

“Mun yi imani cewa wasu ne su ka dauki nauyin wannan ta’adi. Ranmu ya baci sosai.” Inji Rufai.

Dazu kun ji cewa kakakin gamayyar kungiyoyin, CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa 'yan jarida cewa zasu dauki mataki game da matsalar tsaro.

Abdul-Azeez Suleiman ya ce za su shirya tattaki tare da yin gangami a Daura na #Bringbackourboys domin ganin an ceto yaran da aka sace.

Idan za k tuna, 'yan bindiga sun kai hari a wata makarantar sakandare a Kankara, sun sace yara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel