Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria

Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria

- Wata matashiya yar Najeriya ta haifar da zazzafan muhawara a shafin Twitter bayan ta bayar da wani shawara a kan auren mai mata

- @IlhamSafiyyat ta ce auren mai mata shine zabi mafi kyau da budurwa za ta iya yi

- A cewar matashiya, daga cikin tarin alkhairan da ke tattare da hakan shine samun yar’uwa

Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @IlhamSafiyyat ta bayyana cewa auren namiji mai mata shine zabi mafi kyau saboda abubuwa da dama da ke tattare da hakan.

@IlhamSaffiyat ta bayyana cewa irin wannan aure na zuwa da garabasa; ga miji sannan ga yar’uwa.

Yar’uwa da take nufi a nan shine matar da sabuwar amaryar za ta je ta tarar a gidan mijin.

Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria
Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria Hoto: @IlhamSafiyyat
Asali: Twitter

Mutane da dama sun yi martani a wallafar da matashiyar tayi yayinda suka bayar da nasu ra’ayin kan yadda aure ya kamata ya kasance da kuma irin mutumin da mace za ta zaba.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari ba Allah bane, za mu yi masa gyara a inda ya kama, In ji Kashim Shettima

Yayinda wasu suka caccaketa akai, wasu yan tsiraru sun yarda da shawararta.

Kalli wallafarta a kasa:

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya garzaya kasar Amurka don ganin likita

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@Sir_Babex ya ce:

"Allah ya yi maki albarka a kan wannan fahimta taki. Ki ji ma, idan Allah ya yarda sai kin auri mai mata uku, domin ki samu tarin garabasa.”

@khalidGabary ya ce:

"Kawai ki fada mana cewa da mai aure kike soyayya.”

@Obasteve91 ya ce:

"Ba a kasar Yarbawa ba. Za ki shirya wa kanki da yaranki da basu ji ba basu gani ba gadar kiyayya.”

@Nasir1on1 ya ce:

"Bugu da kari za ki zama mata ta lokaci zuwa lokaci: Kwana biyu da miji sannan kwana biyu babu miji. Wani dadi ke cikin haka!”

@KabiruIyayi ya ce:

"Kin yi gaskiya, ci gaba biyu kenan.”

A wani labarin na daban, mun ji cewa an yi taro cikin walwala da annashuwa yayinda Aziza Dangote ta auri burin ranta Aminu Waziri a wani yanayi da za a iya kira da hadadden biki.

Kyakkyawar amaryar ta kasance diya ga Sani Dangote, wanda ya kasance mataimakin Shugaban kamfanonin Dangote tare da yayansa, Aliko Dangote.

Masoyinta, Aminu ya fito shar dashi cikin dakakken shadda dinkin babban riga yayinda Aziza ta fito cikin hadaddiyar dikin doguwar riga inda ta lullube kanta da mayafi shigen kayanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel