Dasuki ya magantu a kan zargin hada baki da Buhari lokacin da ya ke tare da Jonathan

Dasuki ya magantu a kan zargin hada baki da Buhari lokacin da ya ke tare da Jonathan

- Sambo Dasuki ya karyata rade radin da ake yi na cewar ya yiwa Buhari aiki a karkashin kasa a lokacin da yake yiwa Jonathan aiki

- Dasuki ya dai ce ya taba shiga cikin maganar hadakar jam'iyyun hamayya gabanin zaben 2011 amma ya bar tafiyar bayan da aka gama zabe

- Ya tabbatar da cewa, bai taba cin amanar Jonathan ba kasancewarsa mutum mai dakko sabanin yadda wasu ke yadawa a kafofin sadarwa

Tsohon mai bada shawara kan sha'anin tsaro na kasa, Sambo Dasuki, ya karyata rade radin da ake yi na cewar yana yiwa shugaban kasa Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) aiki a karkashin kasa a lokacin da yake yiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan aiki, a matsayin mai bashi shawara kan sha'anin tsaro.

Dasuki ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai taken, 'Ban taba yiwa jam'iyyar APC ko Buhari aiki a karkashin kasa ba a lokacin da nake NSA na shugaba Jonathan.'

Jaridar The Punch ta ruwaito Dasuki a sanarwar yana cewa, "Gaskiyar lamarin shine, na sa hannu a wani yunkuri da akai na hadakar jam'iyyun Action Congress of Nigeria, All Nigeria Peoples Party da kuma Congress for Progressive Change, da sauran wasu jam'iyyu, gabanin zaben 2011, yunkurin da bai yiyu ba.

"Tsoma hannuna a wannan lamarin na hadakar jam'iyyun ya kare bayan da aka gama zaben 2011.

KARANTA WANNAN: Magu: Falana ya yi barazanar shigar da karar wata jarida cikin sa'o'i 48

Dasuki ya magantu a kan zargin hada baki da Buhari lokacin da ya ke tare da Jonathan
Dasuki ya magantu a kan zargin hada baki da Buhari lokacin da ya ke tare da Jonathan
Asali: UGC

"Har zuwa lokacin da na karbi takardar shaidar kama aiki a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a 2012, na sanar da Jonathan cewa ina da alaka da shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, Asiwaju Ahmed Tinubu na ACN da kuma Chied Ogbonnaya Onu na ANPP da wasu daga cikin jam'iyyun hamayya, amma wannan alakar tamu ba zata sa na tauye hakkin wannan mukami da aka bani ba.

"A nawa bangaren, ina mai bada tabbacin cewa, ba zan taba cin amanarsa ba. Kuma a matsayina na mutum na gari, ban ci amanarsa ba."

A matsayinsa na wanda ya rike mukamin mai bada shawara kan tsaro daga 2012 zuwa 2015, Dasuki ya jaddada cewa bai yiwa wasu aiki a karkashin kasa a lokacin Jonathan ba, "kamar yadda wasu marasa kishin kasa da son haddasa fitina ke yadawa a kafofin sada zumunta."

WAIWAYE:

Idan ba a manta ba, jaridar Sunday Tribune a cikin shekarar 2011 ta ruwaito cewa, akwai rudani a yunkurin hadakar da jam'iyyar ACN da CPC ke shirin yi a yayin da masu adawa daga cikin jam'iyyun ke shirin ficewa daga hadakar.

Binciken da Sunday Tribune ta yi a lokacin ya yi nuni da cewa a yayin da shuwagabannin jam'iyyun hamayyar guda biyu ke kokarin ganin an samu nasarar hadakar, wasu jam'iyyun hamayyar guda uku sun juya baya ga wannan hadaka, wacce aka shirya yinta domin kawo karshen jam'iyyar PDP a zaben 2015.

Rahotanni a lokacin sun bayyana cewa jam'iyyar PDP mai mulki a lokacin ba ta dauki hadakar a matsayin wata barazana ba, amma wani kwamitin mashawararta karkashin tsohon mataimakin shugaban kasa Alex Akwueme sun shawarci jam'iyyar da ta dauki matakin gaggawa tun kafin lokaci ya kure domin kuwa hadakar babbar barazana ce ga jam'iyyar.

A zaben 2015 ne jam'iyyar APC, wacce ta kunshi hadakar jam'iyyun adawa, ta samu nasarar lashe zaben shugabancin kasar, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama shubagan kasa a karkshin jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel