Hukumar EFCC ta na so a ware Dasuki daga uwar-shari’ar zargin N19.4b

Hukumar EFCC ta na so a ware Dasuki daga uwar-shari’ar zargin N19.4b

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta fadawa babban kotun tarayya da ke Maitama a Abuja cewa za ta bukaci ayi wa Sambo Dasuki shari’arsa dabam.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, hukumar ta na so a banbanta zaman shari’ar Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, da sauran mutane bakwai wanda ake tuhumarsu tare.

Tun 2015 aka fara gurfanar da tsohon Mai ba shugaban kasar Najeriyar shawara kan harkar tsaro a gaban kotu. Ana zargin Sambo Dasuki da lashe wasu kudi da aka ware domin sayen makamai.

A zaman da aka cigaba, babban Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya gabatar da kukansa gaban Alkali mai shari’a Hussein Baba-Yusuf a game da rashin hallarar wanda ake zargi a kotu.

Kanal Sambo Dasuki shi ne na farko cikin jerin wadanda EFCC ta ke tuhuma da laifi amma an gagara ganin shi a kotu. EFCC ta nemi kotu ta cigaba da yin shari’ar ba tare da an ga Dasuki ba.

KU KARANTA: 2019: Lauyoyin Atiku sun yi halartar zaman kotun koli

Sauran wadanda EFCC ta maka a kotu sun hada tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC, Aminu Baba Kusa; da kuma wani kamfani Acacia Holdings Limited and Reliance Referral Hospital.

Babban Lauya Jacobs ya bayyana cewa abin da ya kamata ayi cikin sauki shi ne a ware Sambo Dasuki, wanda ya ki zuwa kotu daga cikin uwar shari’ar domin Alkali yaya cigaba da aikinsa.

Rotimi Jacob SAN ya ke cewa: “Ba za mu makale a wuri guda na shekaru biyu ba tare da an motsa ba. Don haka a zare sunan Dasuki daga shari’ar domin a hukunta sauran wadanda ake tuhuma.”

Lauyan gwamnatin ya ke cewa za a sake maka karar ragowar wadanda ake tuhuma dabam. Ana zargin Sambo Dasuki a duka karar, amma za a zare sunansa saboda a iya yi cigaba da shari'ar.

Kafin a dage shari’ar, Lauyan da ke kare Baba Kusa watau Solomon Umoh SAN ya nuna rashin gamsuwarsa, inda ya ke ganin zare Sambo Dasuki daga karar za ta sa kotu ta gaza yi masu adalci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel