Satar Dalibai: Yadda na tsira inji ‘Dan Makarantar GSSS Kankara da ya iya tserewa

Satar Dalibai: Yadda na tsira inji ‘Dan Makarantar GSSS Kankara da ya iya tserewa

-Daya daga cikin wadanda aka sace a GSSS Kankara ya samu ya tsere

-Osama Aminu Maale ya ce ya kubuta ne a sakamakon rashin lafiyarsa

-Aminu Maale ya tabbatar da cewa dalibai 520 aka sace a Makarantar

Osama Aminu Maale, mai shekara 18 da haihuwa, ya na cikin daliban makarantar GSSS Kankara wanda aka sace a ranar Juma’a da dare.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin, cewa Osama Aminu Maale ya kubuta daga hannun wadannan miyagun ‘yan bindiga da su ka sace su.

A cewar Osama Aminu Maale, yaran makarantar nan ta GSSS Kankara 520 ‘yan bindigan suka sace.

Jaridar ta rahoto Aminu Maale ya na fada wa AFP a hirar da ta yi da shi ta wayar salula: “Gaba daya mu 520 aka dauka daga makarantar.”

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sake hallaka wani a Katsina yayin da Buhari ya ke Daura

Ya ce: “Bayan sun dauke mu, mun tsaya a cikin motar da muke, inda suka sa manyan daliban su kayi kidaya. An kirga 520.”

Adadin da wannan matashin dalibi ya bada ya ci karo da alkaluman da gwamnati ta fitar.

Daga nan ne sai ‘yan bindigan suka raba su gida-gida, a haka ne Aminu Maale da wasu dalibai hudu su ka samu su ka tsere.

“Wani daga cikin ‘yan bindigan ya yi ta duka na lokacin da na gaza cinma sauran saboda rashin lafiyata, hakan ya sa aka bar ni a baya, na samu damar tsere wa.” Inji Maale.

KU KARANTA: Ba mu ga yara 333 ba - Masari

Satar Dalibai: Yadda na tsira inji ‘Dan Makarantar GSSS Kankara da ya iya tserewa
Sojojin Najeriya Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Kawo yanzu Maale ne kawai ake da labarin ya kubuta daga hannun wadannan ‘yan bindiga. Hukumomi sun yi alkawarin fito da duk wadanda ke tsare.

Dazu kun ji cewa an yi ca a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaza zuwa ya duba mutanen Kankara inda aka yi gaba da daliban makaranta.

Shugaba Buhari ya yi zamansa a Daura, ya ki zuwa Kankara, ya yi jajen sace Daliban makarantar, duk da cewa babu nisa tsakanin garuruwan biyu a Katsina.

Ana tunanin Buhari zai karasa Kankara, sai aka ji ya tado tawaga ta ke ta yi jaje daga garin Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel