Lamarin tsaro ya na kara tabarbarewa har kullum a Najeriya inji Sarkin Musulmi

Lamarin tsaro ya na kara tabarbarewa har kullum a Najeriya inji Sarkin Musulmi

-Sa’ad Abubakar III da wasu Sarakunan Najeriya sun tafi ta’aziyya a jihar Borno

-Sarkin Musulmi ya yi tir da halin rashin tsaro da ake ciki bayan harin Zabarmari

-Mai alfarma Sultan ya ba Sojoji shawara su shiga har Sambisa, su mamaye dajin

Mai alfarma, Sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III, ya koka game da yadda sha’anin tsaro yake kara tabarbarewa har kullum a kasar nnan.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar Sarakuna zuwa ta’aziyya a Borno.

Sarkin Musulmin ya yi wa gwamnati da mutanen Borno ta’aziyyar rashin da jihar ta yi kwanakin baya, inda aka yi wa Manoma yankan-rago a Zabarmari.

Sultan ya ce ba ta’aziyya kadai su ka zo yi a jihar Borno ba, yace za suyi amfani da wannan dama domin fitowa su yi Allah-wadai da abin da ke faruwa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta na kokari duk da matsalolin rashin tsaro – Sheikh Jingir

A matsayinsa na shugaban majalisar Sarakuna na kasa, wadanda su ka yi masa rakiya sun hada da Sarakunan Onitsha, Hadejiya, Fika, da kasar Opobo.

“Mun gaji da zubar da jinin mutanen da ake yi da kowace irin rana a kasar. An rasa rayuka da-dama baya, ba za mu iya fadin adadin ran da aka rasa ba.”

Sultan ya cigaba da cewa: “Abin ya zama ruwan dare. Har an saba da hakan, abin magana shi ne ace an wayi gari babu wanda aka kashe a kasar nan.”

Sultan Sa’ad Abubakar II yace sun ba shugabanni shawarwari a kan halin tsaro, ya yi kira ga sojoji su mamaye yankin tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa.

KU KARANTA: Boko Haram: An kai wa ‘Yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar hari

Lamarin tsaro ya na kara tabarbarewa har kullum a Najeriya inji Sarkin Musulmi
Zulum da Sarkin Musulmi Hoto: twitter.com/ProfZulum
Asali: Twitter

Mai alfarman yace a lokacin yana Laftana, ya jagoranci sojoji sun shiga tafkin Chad, a lokacin yace sai da su ka mamaye tsibirorin da ke karkashin Najeriya.

Ku na da labari cewa har a jihar shugaban kasa ta Katsina, ana fama da hare-haren miyagun ‘Yan bindiga da masu garkuwa da mutane har sai an biya kudin fansa.

‘Yan bindiga sun hallaka wani manomi, sanan sun sace wasu yayin da Buhari ya kai ziyara gida.

A jiya ne kuma ku ka ji cewa gamayyar kungiyar Arewa ta shirya taro kan sha'anin tsaro a garin Kaduna, amma wasu ‘yan iskan gari su ka hargitsa wannan taro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel