An kuma kai hari, an kashe wani, an yi garkuwa da mutane 3 a jihar Katsina

An kuma kai hari, an kashe wani, an yi garkuwa da mutane 3 a jihar Katsina

-An kai hare-hare da-dama tsakanin Asabar zuwa Lahadi a jihar Katsina

-‘Yan bindiga sun kashe wani Manomi a Jibia, an kuma sace wasu mutane

-Duk anyi wannan ta’adi ne a lokacin da Shugaban Najeriya ya kai ziyara

Miyagun ‘yan bindiga sun sake yin ta’adi a jihar Katsina, inda suka hallaka wani Bawan Allah, sannan su kayi garkuwa da wasu mutum uku.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, 2020, ta bayyana abin da ya faru.

Jaridar ta bayyana cewa wadannan ‘yan bindiga sun kai hari ne a karamar hukumar Jibia, su ka kashe wani Bawan Allah, Bashir Mandela Jibiya.

Malam Bashir Mandela Jibiya, manomi ne a garin Jibia da ke iyaka da kasar Nijar. Wannan hari na zuwa ne bayan satar ‘yan makaranta a Kankara.

KU KARANTA: Harin Kankara: PDP ta soki Buhari kan watsa wa Mata 'gas'

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a akalla wurare uku tsakanin Asabar zuwa ranar Lahadi a tsakanin garuruwan Katsina.

A harin farko na ranar Asabar ne aka hallaka Bashir Mandela Jibiya. Bayan nan kuma an auka wa wasu matafiya a kan titunan Batsari da kuma Jibiya.

Tsautsayi ta fada wa wadannan mutane ne a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa cin kasuwar mako.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa an sace wani direban mota mai suna Hassan Yardaji, tare da wasu fasinjojinsa mata har biyu a jiya.

KU KARANTA: Za a dawo da yaran makaranta da aka sace inji Ministan tsaro

An kuma kai hari, an kashe wani, an yi garkuwa da mutane 3 a jihar Katsina
Buhari ya zo bikin sallah jihar Katsina Hoto: www.thenigerianvoice.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce dayan harin da aka kai ya fada kan wata mota ne, inda wadanda suke cikinta suka samu suka tsira da rauni a sakamakon harbin bindiga.

A ranar Lahadin nan kun ji cewa wasu mata sun gudanar da zanga zanga a jihar Katsina a kan sace daliban makarantar GSSS Kankara da aka yi.

Wadannan mata sun gudanar da gangamin ne a harabar makarantar da wannan abu ya faru da titunan yankin, domin nuna wa gwamnati fushinsu.

Duk wannan ya faru ne a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo ziyara a Daura.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel