Ana wata ga wata: Ƴan ta'adda sun kai hari kasuwar Gudu, sun kashe mutum ɗaya
- Wasu yan iska sun kai farmaki sanannen kasuwar nan na Gudu da ke birnin Abuja
- An tattaro cewa akalla mutum daya ne ya rasa ransa daga harin yayinda aka caki wani dan kasuwa
- Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya ta ce za ta yi Karin bayani da zaran ta tabbatar da lamarin
Akalla mutum daya ne ya mutu bayan wasu bata gari sun kai hari kasuwar Gudu da ke babbar birnin tarayya, Abuja sannan kuma suka soki wani dan kasuwa.
Lamarin ya afku ne yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba, da rana, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an rufe kasuwar sannan aka tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da zaman lafiya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnonin Arewa sun shiga taron gaggawa
Tun a ranar Talatar da ta gabata ne aka yi ta samun barkewar rikici daga zanga-zangar EndSARS da ke gudana a wasu yankunan da ke makwabtakawa da wajen irin su Apo, Wumba da kuma Waru.
Wata majiya ta bayyana cewa, tuni yan kasuwa suka tsere daga kasuwar mai yawan jama’a a yankin Gudu.
Da aka tuntubi kakakin yan sandan birnin tarayya, ASP Mariam Yusuf, ta ce za ta tabbatar sannan ta yi karin bayani.
KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Ɓata gari sun sake bankawa ofishin ƴan sanda wuta a Lagos
A wani labarin, mun ji cewa don gujewa cigaba da asarar dukiyar gwamnati a jihar Legas, gwamnatin tarayya ta kara yawan jami'an tsaro don kula da dukiyoyin gwamnati da ke jihar.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a safiyar Alhamis, yayin da ake hira dashi a gidan talabijin din Arise wanda The PUNCH suka dauka.
Sanwo-Olu yace shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin da shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, sun kira shi a waya ranar Laraba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng