Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta

Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta

- Har yanzu ba a ga dalibai 668 ba 'yan makarantar sakandaren gwamnati ta Kankara

- Kamar yadda rahotonni suka tabbatar, makarantar tana da dalibai 1074 ne gaba daya

- Duk da dai jiya gwamnan jihar ya ce an ga yawancinsu, a cewarsa yanzu haka saura dalibai 333

Har yanzu ba a ga dalibai 668 na makarantar sakandaren gwamnati ta kimiyya da ke Kankara ba, kamar yadda rajistar makarantar ta nuna.

Daya daga cikin wakilanmu, wanda ya ziyarci makarantar jiya ya tattara bayanai akan yadda al'amarin ya faru, ya ce makarantar tana da dalibai 1,074 a manya da kananun azuzuwanta.

Wata majiya ta ce, "A bangaren kananun azuzuwa, akwai azuzuwa 6, JSS 1A, mai dalibai 58, 1B, mai dalibai 62 da 1C, mai dalibai 64; jSS 2A mai dalibai 74, 2B mai dalibai 79 da 2C mai dalibai 75.

Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta
Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Najeriya na daya daga cikin zakakuran soji a Afrika, Magashi

"A bangaren manyan azuzuwa kuwa akwai azuzuwa 7, SS1A, 97; 1B,108; 1C,106 da 1D, 118. Sai SS2, akwai 2A, 74; 2B, 79 da 2C, 80, wanda idan aka tattara akwai dalibai 1074 gaba daya."

Mazauna Kankara sun ce wani jirgin sama mai dauke da wakilan gwamnatin tarayya ya sauka a titin Katsina, jiya da daddare. Majiyar ta kara da cewa daliban JSS3 dana SS3 basa makarantar, saboda sun gama jarabawoyinsu, don haka basu cikin wadanda aka kaiwa hari.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka samu nasarar ceto dalibai 270 daga makarantar a daren da al'amarin ya faru, sai kuma wadanda suka tsere cikin dajin da daddaren da kuma wadanda iyayensu suka tabbatar da sun isa gidaje. An kirga yawan daliban da aka ceto gaba daya guda 406 a ranar Lahadi da safe.

KU KARANTA: Kasashenmu suna da tsohon tarihin zumunci, Buhari ya taya shugaban kasan Ghana murnar zarcewa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a jiya ya ce har yanzu ba a ga dalibai 333 ba, maimakon 668 da Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, duk wani mai amfani da data a fadin kasar nan ya caccaki gwamnatin tarayya a kan ikirarin rage kudin data da 50%, Daily Trust ta wallafa.

Wata takarda, wacce ministan sadarwa, Dr Isa Ibrahim Pantami ya sanya hannu, yace an rage kudaden siyan data da 50% tun watan Janairun 2020, inda yace maimakon sayar da 1GB a N1000, ya koma N487.18.

Pantami ya ce ma'aikatar NCC ta samar wa wadanda suke sayar da data wannan rangwamen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel