Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga

Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga

- Gwamnan jihar Katsina ya ce yanzu haka ana neman dalibai 333 na makarantar sakandaren Kankara, an samu nasarar ceto sauran

- Ya ce suna bukatar duk iyayen da yaransu suka koma gidajensu su sanar da hukuma don a san yawan wadanda aka yi garkuwa dasu

- Ya sanar da hakan ne lokacin da ministan tsaro da sauran manyan ma'aikatan tsaro suka je Katsina yi masa jaje a ranar Lahadi

A ranar Lahadi gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu ba a ga dalibai 333 ba na makarantar sakandare ta kimiyya da ke Kankara, Punch ta wallafa.

Ya bayyana hakan lokacin da ministan tsaro, janar Salihi Magashi, ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Katsina don yi wa gwamnan jaje a kan satar daliban makarantar sakandare da aka yi ranar Juma'a a jihar Katsina.

Wadanda suka kai ziyarar sun hada da shugaban jami'an tsaro, shugaban sojojin sama da sauransu.

KU KARANTA: Hadimin Buhari ya goyi bayan Zulum da dalilai, ya ce Borno ta samu cigaban tsaro

Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga
Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

Gwamnan ya ce, "Tabbas an ketare jihar da yaran da aka sata daga wuraren kwanansu, saboda akwai yara daga jihohi daban-daban a makarantar.

"Gabadaya daliban guda 839 ne, yanzu muna binciken inda dalibai 333 suke. Har yanzu muna cigaba da gano inda suke, sannan muna kira ga iyaye da su kira kuma su sanar damu idan sun koma gidajensu.

"A yadda labarai suka iso mana, har yanzu ba a ga dalibai 333 ba, muna ta binciken dazuzzukan, sannan muna neman iyayen daliban ko yaran sun gudo gida don mu san yawan daliban da aka yi garkuwa dasu."

Masari ya ce har yanzu masu garkuwa da mutanen basu kira gwamnati ko kuma wani ba dangane da amsar kudin fansa ba.

Ya tabbatar da yadda suka yi iyakar kokarinsu wurin ceto daliban.

Janar Magashi ya tabbatar wa da gwamnan jihar cewa za su bayar da gudunmawa kwarai.

KU KARANTA: Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu

A wani labari na daban, a kan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan makasudin taron da za a yi na NEC.

A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da 'yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel