Satar daliban Katsina: PDP ta magantu a kan watsa wa iyayen yara barkonon tsohuwa

Satar daliban Katsina: PDP ta magantu a kan watsa wa iyayen yara barkonon tsohuwa

- Jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan jifar wasu masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa

- A cewar Jam'iyyar, gwamnati ta nuna rashin tausayi da rashin imani ga iyayen daliban makarantar sakandaren jihar Katsina da aka sace

- A cewar jam'iyyar, duk da shugaba Buhari yana cikin jihar Katsina a ranar, amma ya gaza kare rayukan al'ummar jihar

A ranar Lahadi, jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan amfani da barkonon tsohuwa wurin korar iyayen daliban makarantar sakandaren karamar hukumar Kankara, jihar Katsina, wadanda suka yi zanga-zanga a kan garkuwa da yaransu da aka yi.

A wata takarda da kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondigan ya saki, ya ce an nuna wa iyayen rashin imani kwarai da rashin tausayi karara, duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin jihar, amma duk da haka bai iya kare yaransu daga 'yan ta'addan ba.

Dama a ranar Juma'a 'yan bindiga suka je wata makaranta a jihar Katsina, duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je hutu jiharsa, inda suka yi awon gaba da dalibai 600; al'amarin da ya janyo cece-kuce iri-iri.

Satar daliban Katsina: PDP ta magantu a kan watsa wa iyayen yara barkonon tsohuwa
Satar daliban Katsina: PDP ta magantu a kan watsa wa iyayen yara barkonon tsohuwa. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hadimin Buhari ya goyi bayan Zulum da dalilai, ya ce Borno ta samu cigaban tsaro

Iyayen daliban, wadanda mafi yawansu mata ne, sun fito suna zanga-zanga don neman adalci ga yaransu ranar Juma'a da dare, Vanguard ta wallafa.

Matan sun je harabar makarantar da wasu bangarori na cikin garin suna zanga-zanga rike da takardu kamar 'Wajibi ne gwamnati tayi magana', 'A dawo mana da yaranmu', 'Muna bukatar tsaro a Kankara' da sauransu.

KU KARANTA: Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG

A wani labari na daban, Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya ce harkar tsaron arewa kullum tabarbarewa take yi.

Ogbeh ya jagoranci mutane zuwa Maiduguri don jajanta wa gwamnan a kan kashe-kashen Zabarmari. Fiye da manoma 40 'yan Boko Haram suka kashe a kauyen da ke karkashin karamar hukumar Jere a makonnin da suka gabata, The Cable ta wallafa.

Tsohon ministan ya ce babbar matsalar da ke addabar arewa shine yadda aka mayar da siyasa ta zama hanyar da kowa yake son ya samu kudi da ita. Ya kara da cewa siyasa kuwa bata samar da cigaba a ko ina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel