Ministan tsaro ya bayyana lokacin da za a dawo da yaran makaranta da aka sace

Ministan tsaro ya bayyana lokacin da za a dawo da yaran makaranta da aka sace

- A cewar ministan tsaro, jami'an tsaron da ke jihar Katsina za su maido da dalibai 333 har gidajensu cikin sauki

- Minista Magashi ne ya fadi hakan a ranar Lahadi lokacin da yaje yi wa gwamnan jihar Katsina jaje

- A cewarsa, za su tabbatar an maido da daliban da suke hannun 'yan bindiga nan da sa'o'i kadan

Duk daliban jihar Katsina da aka dauka za su koma gidajensu nan da sa'o'i kadan, a cewar ministan tsaro, Channels TV ta wallafa.

Ministan tsaro, manjo janar Bashir Magashi ya bayar da wannan tabbacin dangane da daliban jihar Katsina wadanda aka yi garkuwa dasu, inda yace tabbas nan da sa'o'i kadan za su koma gidajensu.

Ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi bayan ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Katsina don jajanta wa iyaye da malaman wadanda al'amarin ya shafa, har da gwamnatin jihar a kan garkuwa da daliban.

KU KARANTA: Yajin aiki: Mun cika wa ASUU dukkan alkawurran da muka dauka, FG

Ministan tsaro ya bayyana lokacin da za a dawo da yaran makaranta da aka sace
Ministan tsaro ya bayyana lokacin da za a dawo da yaran makaranta da aka sace. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

Ya fadi hakan ne bayan kwanaki 2 da 'yan bindiga suka afka wa makarantar sakandare ta kimiyya ta gwamnati da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da daruruwan daliban makarantar.

Magashi ya nuna matukar alhininsa dangane da lamarin, inda yace sun yi hakan ne don su dakatar da karatun dalibai.

A cewarsa, cikin sauki jami'an tsaron da ke jihar Katsina za su tabbatar sun dawo da yaran cikin sa'o'i kadan.

KU KARANTA: Zauren Arewa: Siyasa ita kadai ce babbar masana'antar Arewa

A wani labari na daban, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya goyi bayan kalaman gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da yadda ake ta cece-kuce a kan tsaron kasar nan, Borno ta samu cigaba a fannin tsaro a mulkin Buhari.

Lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a, inda suke sukar abinda Zulum yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel