Dino Melaye ya hadu da tsohon shugaba Jonathan a tsaka da rade-radin fitowarsa takarar shugaban kasa a 2023 (hoto)
- Wani hoton Melaye tare da tsohon Shugaban kasa Jonathan ya janyo cece-kuce daga yan Najeriya
- Tsohon dan majalisar ne ya wallafa hoton a Twitter wanda ya nuna sun hadu ne a wajen wani taro
- Koda dai ba lallai ne yana da nasaba da siyasa ba, taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake alakanta Jonathan da yiwuwar sake dawowa shugabancin kasa a 2023
A yayinda ake tsaka da rade radin shugabancin 2023, Dino Melaye, tsohon sanatan Najeriya ya hadu da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Melaye, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), shine ya wallafa hotonsa tare da tsohon Shugaban kasar a shafin Twitter a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.
Koda dai tsohon dan majalisan bai bayar da kowani cikakken bayani game da haduwarsa da Jonathan ba, alamu daga hotunan sun nuna cewa jiga-jigan biyu sun hadu ne a wani taron jama’a.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mata na zanga zanga a Katsina kan satar yaran makarantar GSSS Kankara
Ana ta hasashen cewa wasu yan siyasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na duba yiyuwar tsayar da Jonathan a matsayin magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Lamarin ya kara girmama bayan ziyarar da wasu gwamnonin APC suka kai wa tsohon Shugaban kasar a kwanaki.
Hakazalika, Shugaban PDP, Uche Secondus, a kwanan nan ya ce Jonathan na da damar neman tikitin jam’iyyar a 2023.
Da yake magana kan ko za a kawo tsohon Shugaban kasar don yayi takara a jam’iyyar, Secondus ya ce an kafa kwamiti domin ya duba kokarin jam’iyyar zaben 2019.
Ya ce da zaran kwamitin ya gabatar da rahotonsa, wadanda ke neman kujerar harda tsohon Shugaban kasar na da ikon jefa kwallonsu a raga.
Yan Najeriya sun yi martani a kan ganawar Melaye da Jonathan
Da yake martani a kan hoton da Sanata Melaye ya wallafa, wani mai amfani da shafin Twitter, fakoo (@fakooluwafemi), ya ce:
“Fushina a kan Goodluck Jonathan saukakke ne... Bai tafiyar da mulkin siyasa yadda ya kamata ba wanda shine ya haifar da gwamnati mara alkibla.
“A dukka wadannan, Jonathan na da nasa kuskuren shima. Sai dai, shi ba shugaba mai maitan son mulki bane.”
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya taya Anthony Joshua murnar lashe wasan dambe da yayi a kan Pulev
Wani mai amfani da Twitter, M.s Mainasara (@msmainasara17), ya ce:
“Mun yi kewar gwamnatinka yallabai. Dan Allah ka mika gaisuwana ga Shugaban kasar. Sannan ka fada masa halin da muke ciki a Najeriya. Muna bukatar dawowarsa.”
A nashi martanin, Chima (@holysonchima) yace yana fatan ganin Sanata Melaye ya ba Jonathan hakuri.
Shakka babu Chima na magana ne gane da sukar gwamnatin Jonathan da Mealye yayi a lokacin da yake APC.
A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar Asabar, ya bukaci gwanatin tarayya da ta sanya dokar ta baci saboda matsalar tsaro a kasar nan bayan da yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai masu yawa a Katsina.
A wata sanarwa Atiku ya bayyana cewa dole gwamnati ta fito da sababbin dabaru ta kuma kyale tsofaffi.
"Sace dalibai masu yawa a makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina, abu ne wanda zai kawo cikas a yakin da ake da rashin tsaro a kasar nan, kuma ina Allah wadai," a cewar Atiku.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng