Ka sanya dokar ta baci, sakon Atiku ga Buhari bayan sace dalibai a Katsina
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci don yakar ta'addanci ta kowane hali bayan yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai
- Atiku ya kuma jajantawa iyaye da al'umma da ma gwamnatin Katsina game da wannan iftila'i ya kuma bukaci gwamnati ta fito da sabbin dabarun yaki don murkushe ayyukan ta'addanci a fadin kasar nan
- Babu wani muhimmin kokari har sai an samar da tsaro a yankunan da abin ya shafa, kuma dole gwamnati ta tsaida hankalin ta har sai an kawo karshen wannan matsala, inji Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar Asabar, ya bukaci gwanatin tarayya da ta sanya dokar ta baci saboda matsalar tsaro a kasar nan bayan da yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai masu yawa a Katsina.
A wata sanarwa Atiku ya bayyana cewa dole gwamnati ta fito da sababbin dabaru ta kuma kyale tsofaffi.
"Sace dalibai masu yawa a makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina, abu ne wanda zai kawo cikas a yakin da ake da rashin tsaro a kasar nan, kuma ina Allah wadai," a cewar Atiku.
DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
"Ina jajantawa iyayen yaran da abin ya afkawa da kuma gwamnati da al'ummar jihar Katsina, jihata kuma jihar marigayi mai gidana, Tafida Shehu Musa Yar'adua. Ina addu'ar Allah ya dawo da su cikin koshin lafiya.
"Ina mai kira ga jami'an tsaro da su dauki matakin gaggauta ceto yaran da aka sace, kuma bai kamata mu nade hannun mu zubawa matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a kasar nan. Dole ayi wani abu.
"Saboda haka ina kira ga gwamnati da sanya dokar ta baci da gaggawa a jihohin da yan tawaye da yan bindiga suka addaba, don shirin yakar su ko ta wani hali.
"Don kauracewa kokwanto, dokar da nake magana akai zata tafi bisa tsarin kundin mulkin kasa na 1999, ta hanyar saka dokar ta zata kula da gine ginen gwamnati ba tare da samun matsala ba.
KU KARANTA: Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi
"Hanyar da ake bi tayi sauki da yawa: ba za mu iya yakar ta'addanci ba idan ba mu daina anfani da dabarar da akayi amfani da ita shekaru biyar da suka gabata ba. Sunyi sauki ba za su gamsar ba, kuma an ga haka a sace dalibai a makarantar Kankara.
"Idan muna so a samu nasara, dole mu kirkiri sabbin dabaru. Wanda za su dakatar da makarantun kwana na wucin gadi a jihohin da abun ya shafa, a mayar da su daliban jeka ka dawo har sai komai ya daidaita."
Atiku ya kuma bayyana cewa dole a jibge jami'an tsaro a kowace makaranta don kula da makarantu tsawon awa 24 a jihohin da abin ya shafa.
"Babu wani muhimmin kokari har sai an samar da tsaro a yankunan da abin ya shafa, kuma dole gwamnati ta tsaida hankalinta har sai an kawo karshen wannan matsala."
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng