Katsina: DHQ ta baza sojojin kasa da na sama neman daliban sakandiren Kankara

Katsina: DHQ ta baza sojojin kasa da na sama neman daliban sakandiren Kankara

- Da sanyin safiyar ranar Asabar ne rahotanni suka wallafa labarin yadda 'yan bindiga suka kai hari wata makarantar sakandire a Katsina

- 'Yan bindiga sun dira dakin kwanan dalibai da ke makarantar sakandiren kimiyya a Kankara tare da yin awon gaba da su

- A yayin da rahotanni suka bayyana cewa wasu daga cikin daliban sun dawo, har yanzu da dama sun bace

Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta baza sojojin kasa da na sama domin nemowa da kuma kubutar da daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara, jihar Katsina, da 'yan bindiga suka sace, kamar yadda HumAnge ta rawaito.

HumAngle ta rawaito cewa kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A wasu 'yan shekaru da suka gabata ne rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sansani na musamman (FOB) a Katsina da kuma wata cibiyar mayar ta martanin gaggawa (QRW) a Daura.

KARANTA: FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu

An kafa cibiyoyin ne domin su taka muhimmiyar rawa wajen yakar da 'yan bindiga da sauran miyagun 'yan ta'adda.

Katsina: DHQ ta baza sojojin kasa da na sama neman daliban sakandiren Kankara
Katsina: DHQ ta baza sojojin kasa da na sama neman daliban sakandiren Kankara
Asali: Twitter

Dakarun rundunar sojin sama daga cibiyoyin za su taimaka wajen neman daliban ta hanyar amfani da jiragen sama na musamman masu na'urorin leken asiri.

KARANTA: Ya samu nakasa; mayakin Boko Haram ya fallasa gaskiyar halin Shekau ke ciki

Isah Gambo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya sanar da cewa tuni an fara bincike da bin sahu domin gano dukkan sauran daliban da har yanzu ba'a san inda suke ba tun bayan harin 'yan bindigar.

TheCable ta yi ikirarin cewa majiyar jami'an ta sanar da ita cewa har ya zuwa yammacin ranar Asabar ba'a san makomar dalibai 345 ba, ba'a san inda suke ba.

Legit.ng ta wallafa cewa sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar Katsina.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng