Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina

Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina

- Wani mai goyon bayan Shugaba Buhari ya dawo daga rakiyarsa kwana hudu bayan yayi tababa da yan adawa a shafin sada zumanta bayan yin garkuwa da yan uwansa biyu

- Mutumin ya wallafa cewa yana tare da Buhari har zuwa sanda wa'adin mulkinsa zai kare a 2023 kafin daga bisani ya goge wallafar bayan garkuwa da yan uwansa a Katsina

- Yayi wani martani wanda ya bukaci shugaban yayi murabus a kasan wani rubutu da ke jin ra'ayoyin mutane akan ko Buhari ya yi murabus saboda matsalar tsaro

Kwana hudu bayan ragargazar yan adawa da bayyana goyon baya ga shugaba Muhammadu Buhari, Usman Rabiu, ma'abocin shafin sada zumanta, ya bukaci shugaban kasa yayi murabus.

Ranar 8 ga Disamba, Rabiu ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa yana goyon bayan shugaban kasar har zuwa lokacin da wa'adin sa zai kare a 2023, ya na sukar wanda ya bayyana a matsayin "wawaye".

Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina
Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu

"Muna tare da Baba har 2023. Wawaye su ci gaba da wawancin su," ya wallafa.

Bayan kwana hudu, Rabiu ya wallafa cewa yan uwansa guda biyu na cikin wanda aka yi garkuwa dasu a makarantar sakandare ta Ƙanƙara a Katsina.

Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina
Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina. Hoto: @iam_UsmanRabiu
Source: Twitter

"Yan uwana biyu na cikin daliban da aka sace," ya wallafa.

Yan bindiga sun afka makarantar a ranar Juma'a, ranar da shugaban kasa ya kai ziyara Katsina, jihar sa ta haihuwa, ziyara ta farko a 2020.

Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina
Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina. Hoto: @iam_UsmanRabiu
Source: Twitter

Wata majiyar tsaro ta shaidawa The Cable cewa dalibai sama da 300 sun bace bayan harin.

Buhari ya bayyana harin a matsayin abin bakin ciki, ya kuma roki a ci gaba da bawa jami'an tsaro hadin kai don kawo karshen ta'addanci.

KU KARANTA: Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi

Da yake sharhi game da wani rubutu da ke tambayar ko ya dace Buhari yayi murabus saboda matsalar tsaro a kasar nan. Rabiu ya bukaci Buhari ya gaggauta sauka.

Wani mutum Mumin Oladipo ya bayyana abin da ya faru da Rabiu a matsayin darasi, kuma ya amince da hakan.

"Wannan darasi ne ga masu nuna soyayya ga Buhari saboda rashin iya mulkin sa bai shafe su ba. Maganar gaskiya bama ganin laifin Buhari har sai abin ya shafe mu," Oladipo ya wallafa.

Rabiu yayi martani: "gaskiya ne."

Rabiu ya soki Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, wanda ya wallafa cewa Buhari ya umarci jami'an tsaro da su bi bayan masu garkuwar.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin yan bindiga kan makarantar sakandire, da ke kankara a jihar Katsina, ya kuma umarci sojoji da yan sanda da su bi bayan maharan su kuma tabbatar da ba wanda aka cutar ko ya bata a cikin daliban," Shehu ya wallafa.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel