Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi

Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi

- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019 Peter Obi ya ce mutum miliyan 11 suka karu cikin masu fama da talauci a kasar nan

- Bankin duniya ya fitar da rahoto, ku je ku karanta wannan rahoto, a wannan shekarar, yan Najeriya miliyan 11 za su fada talauci, inji Peter

- Ya bayyana hakan ne a wani taron jam'iyyar PDP na shiyyar kudu maso gabas a ranar Juma'a 11 ga watan Disamba

Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Peter Obi ya ce adadin talakawa a Najeriya zai kai miliyan 110 zuwa karshen wannan shekara ta 2020.

Ya bayyana haka ranar Juma'a a Akwa, babban birnin jihar Anambra lokacin taron jam'iyyar PDP shiyyar kudu maso gabas don tunkarar babban zabe mai gabatowa na 2023, Channels tv ta ruwaito.

Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi
Adadin talakawan Nigeria zai kai miliyan 110 a ƙarshen shekarar 2020, inji Peter Obi. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: UGC

KU KARANTA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

"Kasar ku tana tangal-tangal, tana nutsewa, kuma idan ba ku dauki mataki ba, abun a kan ku zai kare," inji Obi.

"Bankin duniya ya fitar da rahoto, ku je ku karanta wannan rahoto. Iya wannan shekarar, yan Najeriya miliyan 11 za su fada talauci.

"Wannan miliyan 11 kari ne akan miliyan 100 da ake da su. Wannan ya na nufin a karshen shekara, Najeriya zata samu sama da mutane miliyan 110 da suke rayuwa cikin talauci. Yana da muhimmanci a sani cewa daga cikin miliyan 11 nan, miliyan 8 matasa ne."

KU KARANTA: Zulum ya roƙi Buhari ya tallafawa ƴan gudun hijira 200,000 su koma gidajensu

A na shi jawabin, shugaban PDP na kasa, Uche Secandus ya yi kira da matasa su rungumi sana'a, kuma ya ce nan gaba komai yana hannun su.

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar su ta kirkiri hanyoyi don tallafawa matasa a fadin Najeriya.

A wani labarin daban, mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankinsa.

Safra, wanda kiyasin dukiyar ya kai kimanin $23.2 biliyan, wanda ya zo na 63 cikin jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta fitar.

An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, yayi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel