Buhari ya naɗa shugaban wucin gadi a NDDC
- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya naɗa sabon shugaban wucin gadi a hukumar NDDC
- Kakakin shugaban ƙasa ya ce an zaɓi Effiong Ikon Akwa a matsayin shugaban wucin gadin
- Sanarwar ta ce Akwa zai cigaba da jagorancin hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi
Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Effiong Ikon Akwa matsayin shugaban wucin gadi a Hukumar Cigaba ta Yankin Neja Delta (NDDC).
Kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce Mista Akwa zai cigaba da shugabancin hukumar har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin almundahar kuɗi.
DUBA WANNAN: Ka sanya dokar ta baci, sakon Atiku ga Buhari bayan sace dalibai a Katsina
Kafin wannan naɗin, Akwa ne shugaban sashin kuɗi da harkokin shugabanci a hukumar.
Adesina ya ce shugaban na wucin gadi kwararren Akanta ne kuma lauya a kotun ƙoli ta Najeriya.
KU KARANTA: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
Ya ce an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙararrakin da kwamitin kula da ayyuka na hukumar ta shigar a baban kotun Abuja.
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng