Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara

Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara

- Daliban makarantar GSSS Kankara sun yi bayani filla-filla kan halin da suka tsinci kansu a ciki bayan harin da yan bindiga suka kai masu

- Wani dalibi ya ce a lokacin da suka fara jin harbe-harbe sun zata tashin duniya ne yayi

- Har ila yau wani dalibi ya ce shi yana zaton yan bindigan sun so kashe su ne gaba daya kawai don su shiga kanen labarai

Daliban makarantar makarantar sakandare ta kimiyya ta wamnati da ke Kankara, jihar Katsina, a jiya Asabar sun bayar da bayanin yadda suka shafe tsawon dare a daji biyo bayan harin da yan bindiga suka kai makarantarsu a daren ranar Juma’a.

Har yanzu ba a ga da yawa daga cikin daliban ba yayinda iyayensu suka ce suna cikin damuwa. Sun yi kira ga hukumomin da suka dace a kan su ceto masu yayansu.

Mun dai ji cewa daruruwan Babura dauke da yan bindiga masu muggan makamai sun kai hari makarantar kwana ta maza da ke garin Kankara da daddare.

Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara
Harin yan bindiga: Yadda muka shafe tsawon dare a daji, Daliban GSSS Kankara Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

A yayin harin, daruruwan dalibai sun tsere ta katangar makarantar a yayinda suke neman mafaka domin yan bindigar na ta harbi da neman daliban da suka tsere su dawo.

Harin ya wakana ne yan sa’o’i bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Katsina sannan ya garzaya Daura, mahaifarsa don yin ziyarar sada zumunci na mako guda.

KU KARANTA KUMA: Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa iyaye mata sirrukan su

Harbe-harbe kamar a mafarki

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani dalibin SS1, Kabiru Isah, wadanda ya kasance cikin wadanda suka kwana a jeji bayan sun gudu, ya ce dukka lamarin ya zo kamar a mafarki.

A cewarsa, “Mun bar ajujuwanmu bayan karatunmu na dare da misalin karfe 9:30 na dare sannan muka koma dakunan kwananmu.

“Da misalin karfe 10.30 na dare yayinsa tuni wsunmu suka kwanta, kawai sai muka fara jin harbin bindiga, sai ga manyan dalibai sun rugo suna tashin mutane.

“A yayin da wasu daga cikinsu ke cewa ya kamata mu gudu don neman tsira, wasunsu kuma na cewa kamata ya yi mu taru a dakunan kwanan mu fara fahimtar lamarin tukunna kafin daukar mataki na gaba.

“Yayin da muka ji harbe-harben na kara matsowa kusa, sai muka tunkari katangar makarantar muka tsallaka cikin daji.

“Daga nan ne sai ’yan bindigar suka fara kiran mu cewa babu abin da zai same mu, amma daga karshe sun karbi kudi da wayoyi a hannun wadanda suka makale a makarantar.”

“Mun yi gudu na kimanin awanni uku a cikin dajin, kafin muka taru a wani wuri karkashin bishiyoyi muka zauna a farke har sai lokacin da muka fara jin kiran sallar Asuba.”

Ya ce yan bindigar sun kwace kudade da wayoyin sauran da suka rage a makarantar.

Kabiru ya bayyana cewa mafi akasarin daliban sun ji rauni yayin tsallake Katanga da gudun shiga motar bas.

“Yawancinmu mun samu raunuka yayin tsallake katangar da kuma lokacin da muke gudu a cikin daji, amma mun gode wa Allah mun dawo gida sai dai mun samu labarin cewa maharan sun yi awon gaba da wasu daga daliban,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

Wani babban dalibi wanda bai son a ambaci sunansa, ya ce lamarin da ya afku a daren Juma’a tamkar a fim ne.

“Wasunmu sun zata tashin duniya ne ya zo...Harbin sun kasance tamkar saukar aradu. Ina ganin maharani sun so kashe kowa ne, kila saboda su shiga kannen labarai domin a matsayin dalibai, bamu da abun basu.

“Kuma kusan dukkanmu yaran talakawa ne don haka ina ta al’ajabi ko za su yi garkuwa damu ne don kudi ko kuma kawai kashemu suke son yi yadda suke kashe mutane ba tare da kowani dalili ba,” in ji shi.

Wani dalibi da ya bayar da sunansa a matsayin Yunusa, ya ce: “Mun yi gudu tsawon sa’o’i a jeji. Koda mun so tsayawa, bamu da zabi illa mu ci gaba saboda mun tsorata. Lokacin da muka gaji ne ma wasunmu muka taru a karkashin wani bishiya muna jiran wayewar gari."

A wani labarin, mun ji cewa rundunar sojojin Najeriya da taimakon dakarun sama sun yi nasarar gano mabuyar ƴan bindigan da suka kai farmaki makarantar sakandare na kimiya ta gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina.

An gano cewa ƴan bindigan sun boye ne a dajin Zango/Paula da ke karamar hukumar ta Kankara harma an yi musayar wuta tsakaninsu da sojoji.

Kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ya saki wanda Legit.ng ta gano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel