Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa iyaye mata sirrukan su

Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa iyaye mata sirrukan su

- Mai fafutukar kare hakkin dan adam Aisha Yesufu ta ce duk ma’auratan da ke sanar da iyayensu mata abunda ke wakana a gidajensu toh ta kare masu

- A cewar Aisha, ya zama dole ma’aurata su koyi boyewa iyayensu mata sirrikan aurensu idan har suna so yayi karko

- Yayinda wasu yan Najeriya suka yarda da shawarar matar, wasu sun nuna rashin amincewarsu

Matar nan da ke fafutukar kare hakkin dan adam, Aisha Yesufu, ta je shafin soshiyal midiya domin shawartan ma’aurata a kan su dunga boyewa iyayensu mata sirrikan gidan aurensu idan har suna so yayi karko.

A cewar Aisha, akwai matsala idan har ma’aurata suka fara sanar da iyaye mata abunda ke gudana a gidajensu.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun gano inda ƴan bindiga suka ɓoye ɗaliban GSSS Kankara, anyi musayar wuta

Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa surukai sirrukan su
Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa surukai sirrukan su Hoto: @AishaYesufu
Source: Twitter

Ta wallafa cewa:

“Idan kayi aure, mutum na farko da ya kamata ka tabbatar da ka boye wa sirrin gidan aurenka itace MAHAIFIYAR KA! Wadannan nan soyayya da kulawar da son sanin ko komai na tafiya daidai duk da sunan soyayya? Akwai matsala! Kana fara sanar da ita abunda ke wakana toh ta kare maka! Sai su fara shiga sharo ba shanu!

"A matsayin sabbi aure, ku koyi abunda zai fisshe ku. Abu na daban ne. Ku gina shi da kanku yadda kuke so. Ku fitar da kowa daga cikinsa! Ku yi abunku kuma ba abu mai sauki bane kulla auren mutane biyu mabanbanta. Don haka ku dauki lokain ku. Ku fitar da kowa daga ciki kuyi son ranku."

Mutane da dama sun je shashin yin sharhi domin sanar da ra’ayinsu yayinda wasu suka yarda da ita, wasu kuma sun nuna rashin amincewarsu.

Wani mai amfani da Twitter @Egi_nupe_ ya rubuta:

“A koda yaushe yana da matukar wahala domin iyaye mata na yin hakan ne saboda soyayyarsu ga yaransu.”

@koladechris ya rubuta:

“Ka boyewa mahaifiyarka sirrin aurenka a kan wani dalili? Wannan kwata-kwata baya bisa turba. Shin Aisha Yesufu ta yi nasarar hana mahaifiyarta da sirikarta shiga lamuran aurenta?”

@RilCeeJay ya yi martani da:

“Kada ki yi fushi yaruwa amma b azan taba daukar aurena da muhimmanci fiye da mahaifiyata/iyayena ba. Bugu da kari ba zan taba auren yariyar da mahaifiyata bata yi na’am da ita ba. Ba zan taba zama tushen bacin ran mahaifiyar da ta kawoni duniyarnan ba saboda na samu abar so. Sam, ba dani ba!”

KU KARANTA KUMA: Hazikan sojojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram, sun kashe guda 9

A wani labari, wata likita yar Najeriya mai suna Dakta Halima Abubakar ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure.

Matashiyar budurwar ta wallafa wani kyakkyawan hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure.

Tuni bangaren sharhi na wallafar tata ya cika da martani daga mazan Najeriya wadanda suka nuna ra’ayi a kanta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel