Garkuwa da ɗalibai: Masari ya zubar da hawaye yayinda ya ziyarci Ƙankara

Garkuwa da ɗalibai: Masari ya zubar da hawaye yayinda ya ziyarci Ƙankara

- Aminu Bello Masari, gwamnan Jihar Katsina ya ziyarci makarantar sakandare ta maza da ke Kankara inda 'yan bindiga suka sace dalibai

- Gwamna Masari ya zubar da hawaye yayin da ya ke rokon mazauna garin su yi hakuri a yayin da gwamnati ke kokarin ceto yaran

- Gwamnan ya ce sojoji sun sanar da shi cewa suna fafatawa da 'yan bindigan kuma ya bada tabbacin za suyi iya kokarinsu don ceto dukkan daliban

Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya ce babu wanda ke da tabbas kan adadin daliban makarantar sakandare da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace a karamar hukumar Kankara a jihar, SaharaReporters ta ruwaito.

A daren ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka afka Makarantar Sakandarin Kimiyya da Maza da ke Kankara suna ta harbe harbe sannan suka yi awon gaba da dalibai masu yawa.

Garkuwa da dalibai: Masari ya zubar da hawaye yayin ziyarar da ya kai Kankara
Garkuwa da dalibai: Masari ya zubar da hawaye yayin ziyarar da ya kai Kankara. Hoto: @SaharaReporters
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu

Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Asabar yayin da ya ziyarci makarantar, Masari ya ce gwamnatin jihar na kokarin ceto daliban.

Gwamnan cike da tausayi kan abinda ya faru, ya zubar da hawaye yayin da ya ke rokon mazauna garin suyi hakuri yayin da gwamnati ke kokarin ceto yaran.

Ya basu tabbacin cewa gwamnati za tayi duk abinda ya kamata domin ganin an ceto dukkan daliban da aka sace.

KU KARANTA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

Masari ya ce, "Wannan babban abin bakin ciki ne, kuma muna iya kokarinmu don ganin an ceto daliban. Ba zamu iya cewa mun fi iyayen damuwa ba amma tabas muna cikin bakin ciki don mun san hakkin mu kare su.

"Sojoji sun sanar da ni cewa a halin yanzu suna fafatawa da 'yan bindigan, kuma za muyi iya kokarin mu don ceto su duka. Mun bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana sannan a mayar da yara gidajen iyayensu."

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel