Mawallafin Jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah ya rasu
- Mawallafin Jaridar Leadership Newspaper, Mista Sam Nda-Isaiah ya riga mu gidan gaskiya
- Ya rasu ne misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma'a bayan ya koka cewa baya jin daɗin jikinsa
- Nda-Isiah ya hallarci taron kungiyar masu jaridu, NPAN, a Legas a ƙarshen makon da ta gabata
Allah ya yi wa mawallafin Jaridar Leadership, Mista Sam Nda-Isaiah rasuwa yana da shekaru 58 a duniya.
Majiyoyi sun bayyana wa The Nation cewa marigayin ya rasu misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma'a bayan ya koka kan cewa baya jin daɗin jikinsa.
DUBA WANNAN: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya
Nda-Isiah ya hallarci taron kungiyar masu jaridu ta Najeriya, NPAN, a jihar Legas a ƙarshen mako.
Marigayin wanda haifaffen jihar Niger ne ya yi karatun digiri a fannin kimiyyar magunguna a Jami'ar Ife.
Ya kuma taɓa neman tikitin takarar kujerar shugabancin ƙasa a jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Wani daga cikin iyalansa ya shaidawa wakilin jaridar Punch a wayar tarho cewa:
"Eh, da gaske ne. Yanzu aka sanar da ni."
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja
A lokacin hada wannan rahoton, babu sanarwar rasuwarsa a shafin jaridar ta Leadership.
Sai dai wasu daga cikin fitattun mutane ciki har da kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi ta'aziyar rasuwarsa.
An haife shi a shekarar 1962 a Minna, Jihar Niger. Mista Nda Isaiah kuma yana da sarautar Kakakin Nupe a jihar Niger.
A wani labarin daban, mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankinsa.
Safra, wanda kiyasin dukiyar ya kai kimanin $23.2 biliyan, wanda ya zo na 63 cikin jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta fitar.
An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, yayi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng