COVID-19: Kungiyoyi suna kiran taron addini da ake samun cinkoso inji PTF

COVID-19: Kungiyoyi suna kiran taron addini da ake samun cinkoso inji PTF

-Kwamitin PTF ya zargi kungiyoyin addini da laifi wajen yaduwar COVID-19

-A halin yanzu cutar ta sake dawo wa, ta na harbin mutane a jihohin Najeriya

-Boss Mustapha ya ce ana saba ka’ida wajen kiran taron addini, ana cincirindo

Kwamitin PTF mai yaki da annobar COVID-19 a Najeriya ya zargi wasu kungiyoyin addini da saba dokoki da sharudodin da aka gindaya a kasar.

PTF ya yi wannan magana ne bayan an fara samun karuwar masu dauke da cutar a cikin ‘yan kwanakin nan, inda lamarin ya yi kamari sosai.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, 2020, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya zargi malamai.

Mista Boss Mustapha ya shaida wa ‘yan addini cewa kungiyoyin addini sun rika kawo cikas ta hanyar tara jama’a ba tare da la’akari da ka’idoji ba.

KU KARANTA: Manyan da su ka mutu a Najeriya a 2020

Mustapha ya yi wa manema labarai yadda annobar ta yi tasiri a al’umma ta hanyar jawo rikici, tabarbarewar lafiyar kwakwalwa da shan kwayoyi.

Boss Mustapha yace PTF na aiki da masu fada a ji da masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan wadanna matsaloli da ake fuskanta dalilin annobar.

Jaridar The Nation ta rahoto SGF ya na cewa: “Mun lura cewa, abin takaici, ‘yan Najeriya, musamman kungiyoyin addini, sun cigaba da shirya manyan taro da ke iya yada cutar.”

"PTF ta na kira ga duk kungiyoyin kasa cewa babban nauyi ne a kansu su tabbatar an bi doka da sharudan da aka gindaya domin hana yaduwar cutar.” Inji Mustapha.

KU KARANTA: Satar kayan tallafin COVID-19 ya wanke Buhari

COVID-19: Kungiyoyi suna kiran taron addini da ake samun cinkoso inji PTF
'Yan kwamitin PTF Hoto: facebook.com/osgf.gov.ng
Source: Facebook

Yayin da ta ke shirin gabatar wa shugaban kasa rahoton karshe, PTF ta gargadi jama’a game da cinkoso lokacin biken kirismeti da bikin sabuwar shekara.

A jiya da yamma kun ji cewa Masanan Duniya su na ganin watakila matsin tattalin arzikin Najeriya ya dore har shekarar 2023 idan ba a tashi tsaye ba.

World Bank Nigeria Development Update ta ce babu wani tabbacin cewa tattalin arzikin Najeriya da ya sukurkuce kwanan nan zai dawo daidai a cikin 2022.

Bayan haka, ana tunanin yawan Talakawa zasu karu da miliyan 20, kuma za a iya yin yunwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel