Yanzu-yanzu: Yan sanda sun kwato sandar ikon majalisa da aka sace

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun kwato sandar ikon majalisa da aka sace

- Kamar yadda akayi da na majalisar dattawa a baya, an kwato sanda ikon majalisar Ogun

- Wasu batagari sun fasa cikin majalisar ranar Alhamis suka dauketa

- Ba tare da bata lokaci ba sun garzaya da ita jihar Legas

Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun samu nasarar kwato sandar ikon majalisar dokokin jihar Ogin da aka sace ranar Alhamis.

Yan sandan dake ofishin Trade Fair sun kwato sandar ne a unguwar Abule Ado a jihar Legas.

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun kwato sandar ikon majalisa da aka sace
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun kwato sandar ikon majalisa da aka sace
Source: Twitter

KU KARANTA: Karya ne, ba kashesu akayi ba, hadari suka yi: Gwamnatin Kaduna kan mutuwan yan Kano 16 (Hotuna)

KU DUBA: Malaman addini na kawo mana matsala, Sakataren gwamnatin tarayya

A jiya mun kawo muku rahoton cewa wasu yan baranda a ranar Alhamis sun kai hari majalisar dokokin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da sandar iko na majalisar.

Kakakin majaisar dokokin jihar, Olakunle Oluomo ya ce matasa sun fasa cikin majalisan ne da safiyar Alhamis kuma suka dauke sandar.

Ya ce amma an samu kwato kan sanda dake dauke da tambarin Najeriya, har yanzu ana neman sauran jikin.

An kaddamar da bincike kan wadanda suka aikata hakan da wanda ya turo su, ya kara.

Olakunle Oluomo, ya tabbatar da aukuwan hakan amma ya ce sace sandar ikon bai da alaka da siyasa.

A hirar da yayi da Channels, ya bayyana cewa barayi ne kawai kuma ta cikin kwanon rufin majalisar suka shigo

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel