Malaman addini na kawo mana matsala, Sakataren gwamnatin tarayya

Malaman addini na kawo mana matsala, Sakataren gwamnatin tarayya

- Mutane sun saki jiki da annobar Korona kuma gashi an koma gidan jiya

- Yanzu haka birnin tarayya Abuja da jihar Kaduna ke kan gaba wajen sabbin masu kamuwa

- Gwamnan jihar Kaduna yayi barazanar sake kafa dokar kulle

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta zargi Malaman addini da laifin sabawa umurninta wajen dakile yaduwar cutar Korona a fadin tarayya ta yadda suke tara jama'a a wuraren ibada.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar, Boss Mustapha, ya bayyana hakan a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Punch ta ruwaito.

Yace, "Mun lura cewa wasu yan Najeriya, musamman kungiyoyin addini sun cigaba da gudanar da shirye-shiryensu da ka iya kara yaduwan cutar."

"PTF na kira ga hukumomin da sukayi yarjejeniya da wadannan kungiyoyin su tashi tsaye don hukuntasu."

A cewarsa, PTF na cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan illolin da cutar COVID-19 irinsu kan kwakwalwa, ta'amuni da kwaya, da kuma cin zarafi.

Mustapha yace ko da an fito da riga-kafi, wajibi ne mutane su cigaba da bin ka'idojin kare kai saboda kowa ya tsira.

KU KARANTA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

Malaman addini na kawo mana matsala, Sakataren gwamnatin tarayya
Malaman addini na kawo mana matsala, Sakataren gwamnatin tarayya Credit: @NCDCgov
Source: Twitter

KU KARANTA: Lai, Gbemisola da Abdulrazaq su na yakin karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara

A bangare guda, Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 675 ranar Alhamis a cewar alkaluman hukumar kiyaye yaduwar cututtuka watau NCDC.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 71,344 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Alhamis , 11 ga watan Disamba, 2020.

A bangare guda, ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.

Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.

Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel