Ku dakatar da dukkan burikanku na 2023, Saraki ya shawarci 'yan siyasa
- Bukola Saraki ya ce duk wanda ya karkatar da hankalinsa wurin neman kujerar 2023 a yanzu, baya da kishin Najeriya
- A cewar tsohon shugaban majalisar dattawa, kasar nan tana cikin mawuyacin hali, kamata yayi a nemi maslaha
- Ya kara da cewa, ya kamata 'yan jam'iyyar PDP su dakata da yakin neman zabe, a fara magance matsalolin tsaron Najeriya
Bukola Saraki, shugaban kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP ya ce yakamata shugabanni su dakata da neman kujeru, su hada kan 'yan kasa, a gyara makarantu sannan su janye duk wasu matsalolin da ke raba kawunan al'umma.
Ya shawarci shugabanni masu neman kujerun siyasa, da su dakata na wucin gadi, a gyara kasar nan tukunna. Yakamata su nuna cewa su 'yan kasa nagari ne, Premium Times ta wallafa.
Saraki ya ce, "Duk wata jam'iyya ko kuma dan siyasa wanda bai damu da matsalar da ke addabar kasar nan ba a wannan lokacin, bai cancanci rike wani mukami ba a kasar nan.
"A yanzu, babu abinda yafi Najeriya muhimmanci."
KU KARANTA: Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce, alamu sun nuna ba nasarar PDP kadai Najeriya take bukata ba don ta farfado ta koma yadda take.
Ya yi wa shugabannin jam'iyyar PDP alkawarin cewa kwamitin sasancin jam'iyyar za su yi iyakar kokarin yin ayyukansu yadda ya dace.
A cewar Saraki, tuni kwamitin ta fara ayyuka a kan yadda za ta nemi hadin kan 'yan jam'iyyar.
"Mun riga mun tattauna kuma mun zauna da gwamnoninmu, wadanda su ne za su jagorancin hadin kan al'umma.
"Ina alfaharin sanar da kowa cewa har yanzu PDP ce kadai jam'iyyar da za ta iya hada kan 'yan Najeriya kuma tayi gyara yadda ya kamata.
"Alamar muhimmancin jam'iyyar shine, ita ce kadai jam'iyyar da take da a kalla ko gwamna daya ne a kaf yankunan da ke kasarn an.
"Sannan jam'iyyar ce kadai take da mai mukami a kowanne yanki, mazaba, kananun hukumomi, jihohi da ko ina a fadin kasar nan," yace.
An sha cewa "Duk wani layi ko anguwa, wanda ba a ga alamar lema ba, ba cikin Najeriya take ba."
A cewar Saraki, duk da akwai alamar a 2023 PDP za ta yi nasara, amma akwai bukatar 'yan jam'iyyar su hada kawunansu don cimma nasara.
KU KARANTA: Boye matar aure: Wata kotu a Kano ta bukaci Rarara da ya bayyana a gabanta
A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zama da 'yan majalisar wakilai don tattaunawa a kan matsalar rashin tsaro, kamar yadda 'yan majalisar suka bukata.
Kamar yadda kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace, an tsayar da ranar da za a tattauna, kuma nan kusa za a sanar da lokacin.
Ya fadi hakan a ranar Laraba, inda yace Shugaban kasa ya fi kowa shiga cikin damuwa a kan yanayin rashin tsaron da kasarsa take ciki, kuma zai yi wa 'yan Najeriya magana ta wurin wakilansu nan kusa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng