Saraki ya ce gaskiya za ta yi halinta kan rushe gidan mahaifinsa

Saraki ya ce gaskiya za ta yi halinta kan rushe gidan mahaifinsa

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yi martani kan rushe wani gida mallakin mahaifinsa a Ilorin da gwamnatin jihar Kwara mai ci yanzu ta yi.

Saraki ya ce nan da ba dade wa ba gaskiya za ta yi halin ta, a cikin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairun 2020 kan rushe gidan mahaifinsa da aka yi.

Ya kuma jinjinawa mutane, yara da manya da suka nuna goyon baya ga marigayi mahaifinsa da iyalansa a kan batun rushe gidan.

Bukola Saraki ya yabawa mutanen saboda nuna masa cewa ana tare.

Ya ce goyon bayan da mutanen suka nuna na nufin cewa ginin na da muhimmanci matuka a gare su.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Najeriya na son kashe mahaifi na - Diyar El-Zakzaky

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya mika godiyarsa ga mutanen bisa kauna da soyaya da suka nuna wa mahaifinsa da iyalansa.

Kazalika, saoi kadan bayan rushe gidan da gwamnatin jihar Kwara ta yi mallakar Olushola, mahaifin tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki, jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana rushe gidan a matsayin zalunci, gidadanci da ragwanci da ka iya haifar da rikici a jihar.

Legit.ng ta ruwaito cewa jamiyyar ta PDP ta zargi gwamnatin na APC a jihar da yi wa yan adawa bita da kulli a cikin sanarwar da sakatarenta na kasa Kola Ologbondiyan ya fitar a yammacin Alhamis 2 ga watan Janairu.

Ta ce kiyaya da zalunci da yunkurin dakile jamiyyar adawa a jihar ne ya sa gwamnatin mai mulki a yanzu ta aikata lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164