Ba zamu koma aji ba sai an biya mana bukatunmu - Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu
- Kungiyar ASUU ta bukaci iyaye da dalibai su fahimci dalilin da yasa suke yajin aiki
- Watanni bakwai kenan da daliban jami'a suke zaune a gida sakamakon yajin malaman
- Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a fadin tarayya
Kasa da sa'o'i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da bude dukkan makarantu, kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta ce malamanta ba zasu koma makaranta ba sai an biya bukatunsu.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa biodun Ogunyemi, ya tunatar da gwamnatin tarayya da iyayen yara cewa lakcarorin sun shiga yajin aiki ne saboda an ki amsa bukatunsu.
Yayinda yake tsokaci kan sanarwan bude makarantu, Ogunyemi ya bayyanawa jaridar Sun cewa "Ba mu muka kulle jami'o'i ba. Hakkin gwamnati ne ta bude. Amma kuma hakkinmu ne mu ki karantar da dalibai."
DUBA NAN: Ana saura kwanaki 11 zabe, Buhari na son baiwa jihar Ondo N7bn
KU KARANTA: Sabbin mutane 126 sun kamu da Korona, yayinda ake gab da isa 60,000
Ogunyemi ya ce kungiyar ta dade tana yaki da gwamnatin tarayya kan kudaden da ake bukata wajen yiwa jami'o'in Najeriya garambawul domin su kara da manyan jami'o'in duniya.
Game da albashinsu kuwa, Ogunyemi ya ce manhajar IPPIS ta haifar da matsaloli da kuma hanyoyin sata da jami'an gwamnati.
A cewarsa, kokarin tilastawa lakcarori rijista a manhajar IPPIS ba tare da amincewarsu ba ya sa mambobinsu basu samu albashi ba na tsawon watanni uku zuwa takwas yanzu.
"Shin kun san wasu mambobinmu basu samu albashi tba un watan Febrairu 2020. Manhajar IPPIS ba zata iya tafiyar da tsarin biyan albashi a jami'o'i ba." Ya ce
Ogunyemi ya yi kira ga dalibai da iyaye su kara hakuri da kungiyar saboda ana wannan yajin aikin ne don inganta jami'o'i.
A bangare guda, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanar da umurnin bude dukkan makarantun Firamare, Sakandare, da jami'o'i a Najeriya.
Adamu ya sanar da hakan ranar Juma'a a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Premium Times ta ruwaito.
Ya bada shawaran cewa dukkan makarantun su bi ka'idojin da aka gindaya na bude makarantu da kwamitin yaki da cutar Korona PTF ta sanar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng