An yi garkuwa da Hakimin Yakila, Malamar jinya da wasu yara biyu a jihar Neja

An yi garkuwa da Hakimin Yakila, Malamar jinya da wasu yara biyu a jihar Neja

- Masu garkuwa da mutane sun je cikin dare sun sace Hakimin Garin Yakila

- Wadannan ‘Yan bindiga sunyi gaba da wata Malamar asibiti da ‘ya‘yanta

- Babu abin da Jami’an tsaro suka iya yi a lokacin da ake wannan aika-aika

Ibrahim Abdulhamid, Mai girma Hakimin garin Yakila, a karamar hukumar Rafi, jihar Neja, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda jaridar This Day ta bayyana a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, 2020, an shiga garin Yakila an sace Hakimin ne a jiya.

Da kimanin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Alhamis ‘yan bindiga suka auka wa kauyukan Yakila da Garin-gabas, suka yi wannan ta’adi.

KU KARANTA: Ya yi kicibis da Mai garkuwa da mutane a mota

Bayan wannan Mai gari, an kuma sace wata malamar jinya da ke aiki a asibitin Garin-Gabas, sunan wannan Baiwar Allah, Malama Halima.

Jaridar ta ce an kuma yi gaba da wasu kananan ‘ya ‘yanta biyu, ana zargin duk an yi garkuwa da su.

Rahotanni sun bayyana cewa kimanin ‘yan bindiga 20 su ka shigo garuruwan a kan babur, dauke da manyan makamai har da bindigoyin AK-47.

“Sun yi ta harbi a iska domin su razana al’ummar garin, hakan ya sa kowa ya ci kafar kare.”

KU KARANTA: Gudun a-ji kunya ya sa aka sa Buhari ya yi magana biyu

An yi garkuwa da Hakimin Yakila, Malamar jinya da wasu yara biyu a jihar Neja
IGP Mohammed Adamu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Wasu daga cikin ‘yan bindigan sun shiga har dakin Hakimi a gidansa, su ka tursasa masa ya bi su.” Inji wani wanda aka yi abin a gaban idanunsa.

Majiyar ta ce mutanen gari da-dama sun tsere sun shiga daji domin su tsira da ransu. Bayan haka, ‘yan bindigan sun saci kayan amfanin gonan jama’a.

Dazu kun ji cewa wasu manya sun huro wuta, sun ce Allan-barin sai an tsige duka Hafsun Sojoji, saboda halin rashin tsaro da ake fama shi a Najeriya.

Fitattun mutane 41 su kayi wa gwamnatin Muhammadu Buhari taron-dangi wannan karo, su na so a nada sababbin Hafsun soji, domin kawo zaman lafiya.

A halin yanzu shugaban kasa na cigaba da fuskantar matsin lamba a kan manyan jami’an tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel