Idan aka cigaba da yajin-aiki, za mu rufe sauran Jami’oi inji Sunday Asefon

Idan aka cigaba da yajin-aiki, za mu rufe sauran Jami’oi inji Sunday Asefon

-Kungiyar NANS ta ce dalibai sun gaji da yajin-aikin da Malaman Jami’a su ke yi

-Shugaban kungiyar Daliban yace za su zauna da shugabannin ASUU da gwamnati

-Sunday Asefon ya ce za su rufe Jami’o’in kudi da ke Najeriya idan abu ya ci tura

Sunday Asefon, sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya, ya sha alwashin rufe jami’o’in kudi na ‘yan kasuwa idan aka cigaba da yajin-aiki.

Jaridar Punch ta rahoto Sunday Asefon yana bayani, yace muddin aka zarce da yajin-aikin da ake yi a jami’o’in kasar, lallai za su dauki mataki.

Shugaban daliban ya bayyana haka lokacin da jaridar ta tattauna da shi a shirin The Roundtable.

A cewarsa, NANS za ta zauna da wakilan gwamnatin tarayya da bangaren shugabannin kungiyar malaman jami’a na ASUU domin a samu mafita.

KU KARANTA: ASUU za ta zauna da bangaren Gwamnati

Kwamred Asefon ya bayyana cewa muddin aka gaza samun mafita bayan NANS ta zauna da gwamnatin tarayya da ASUU, za su rufe makarantu.

“A tarihin ASUU, wannan shi ne yajin-aikin da ya fi kowane tsawo, an yi watanni tara yanzu. Gwamnatina ba ta jin dadin wannan.” Inji Asefon.

“Zamu yi zama da wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyar ASUU domin ganin yadda za a samu maslaha, saboda dalibai su koma makaranta.”

Afeson ya ke cewa: “Dole a samu mafita mai wanzu wa, ASUU ta daina yajin-aiki, gwamnati ta kuma saurari ASUU. Su ji tausayin daliban da ke gida.”

Idan aka cigaba da yajin-aiki, za mu rufe sauran Jami’oi inji Sunday Asefon
Manyan ASUU a taro Hoto: dailytrust.com
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnati ta saba alkawari - ASUU

Ya ce sun gaji da zamam gida, sun kagara a koma karatu, kuma idan abin ya faskara za su tashi su rufe makarantun ‘yan kasuwa inda ‘ya ‘yan manya suke.

Tun a watan jiya kungiyar ASUU ta ce za ta iya koma wa bakin aiki da zarar an biya hakkokin 'ya 'yanta. Har yanzu da mu ke magana, dogon yajin aikin na nan.

Wani shugaban kungiyar ta ASUU, Ade Adejumo ya bayyana haka a madadin malaman jami'an.

Ku na sane cewa wannan yajin-aikin da ake yi, shi ne mafi tsawo da kungiyar ASUU ta yi a Najeriya. Ba yau ne ASUU ta fara yin dogon yajin-aiki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel