Shugaba Buhari ya ƙara matasan da za a ɗiba a N-Power zuwa miliyan ɗaya

Shugaba Buhari ya ƙara matasan da za a ɗiba a N-Power zuwa miliyan ɗaya

- Shugaba Buhari ya amince da kara adadin masu amfana da shirin koyar da sana'a da bada tallafi na N-Power

- Shugaba Muhammadu ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter a ranar Alhamis

- Shugaban ƙasar yace ya dauki wannan matakin ne da nufin cika alƙawarin fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a kara adadin mutane zuwa miliyan ɗaya waɗanda a karkashin shirin bada tallafi na matasa wato N-Power.

Ya kuma amince da faɗada shirin gwamnatin tarayya na tallafawa al'umma na GEEP.

Buhari ya ƙara mutum miliyan ɗaya cikin wanda za su amfana da N-Power
Buhari ya ƙara mutum miliyan ɗaya cikin wanda za su amfana da N-Power. Hoto @NGRPresident
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

Da ya ke bada sanarwar da shafinsa na Twitter, shugaban kasar ya ce an ɗauki matakin ne da nufin cika alƙawarin da ya ɗauka na tsamo yan Najeriya miliyan 100 daga talauci.

A cewarsa, za a ƙara dalibai miliyan biyar cikin tsarin ciyar da yan makaranta na NHGSFP.

KU KARANTA: Ana neman sojojin Nigeria 43 da suka yi batar dabo bayan turasu aiki a Turai

Ya ce, "Muna nan kan bakanmu na shirin tsamo ƴan Najeriya miliyan ɗaya daga talauci. Don haka na bada umurnin faɗa shirin mu na tallafawa al'umma: Za a ninka masu amfana da shirin @npower_ng zuwa miliyan ɗaya; za a ɗauki sabbin masu amfana da @geep sannan sabbin dalibai miliyan 5 za su samu shiga tsarin @NHGSFP."

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel