Da duminsa: Ɗan Maina, Faisal da ake nema ruwa a jallo ya shiga hannu

Da duminsa: Ɗan Maina, Faisal da ake nema ruwa a jallo ya shiga hannu

- Jami'an tsaro sun kama dan Abdulrasheed Maina, Faisal, da ya tsere daga hannun beli

- Bayan tserewarsa ne kotu ta bawa jami'an tsaro umurnin kama shi a duk inda suka ganshi

- Ana tuhumar Faisal da laifuka masu alaka da almundahar kudade da ke da alaka da mahaifinsa

Faisal, dan tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho garambawul, Abdulrasheed Maina ya shiga hannun hukuma, Vanguard ta ruwaito.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tabbatarwa kotu a ranar Alhamis cewa Faisal mai shekaru 24 wanda ya tsere daga beli tun ranar 24 ga watan Yuni ya shiga hannu a daren ranar Laraba.

An gurfanar da shi a kotu ne bisa zarginsa da aikata laifuka uku masu alaka da almundahanar kudade.

Da duminsa: Dan Maina, Faisal ya shiga hannun hukuma
Da duminsa: Dan Maina, Faisal ya shiga hannun hukuma. Hoto @Vanguardngrnews
Source: UGC

DUBA WANNAN: Janar ɗin soja ya mutu bayan kamuwa da korona a Abuja

Mai shari'a Okon Abanga a ranar 24 ga watan Nuwamba ya janye belin da aka bawa Faisal kuma ya bada umurin jami'an tsaro su kama shi duk inda suka ganshi.

Lauyan dan majalisar jihar Zamfara, Umar Dan Galadima da ya tsaya wa Faisal yayin karbar beli ne ya tabbatar wa kotu cewa jami'an tsaro sun kama shi a daren Laraba.

Lauya M.E. Sheriff a ranar Alhamis ya bukaci kotu ta dakatar da shari'ar duba da cewa an kama wanda ya ke karewa.

Duk da cewa ya tabbatar da kama Faisal, lauyan EFCC, Farouk Abdullah ya ce har yanzu ba a mika wa hukumar wanda ake tuhumar ba.

"Ba a mika mana shi ba kawo yanzu, amma mun samu labari (ba a hukumance ba) cewa an kama shi," inji lauyan mai shigar da kara.

A bangarensa, Mista Anayo Adibe, lauya mai kare wanda ake zargi, ya nemi a dakatar da shari'ar "don ya tabbatar da halin da wanda ya ke kare wa ya ke ciki".

KU KARANTA: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

Ana zargin cewa Faisal a tsakanin 2013 zuwa 2019 ya karbi kudin Naira miliyan 58.11 da ake zargin na rashawa ne daga mahaifinsa Maina.

Ana kuma zarginsa da rashin bayyana wa hukumar EFCC kadarorinsa.

Rahotanni sun ce Faisal ya ciro bindiga ya kallubalanci jami'an DSS da suka tafi kama mahaifinsa a wani otel a Abuja a ranar 30 ga watan Satumba.

Shima Maina an kamo shi a kasar Nijar bayan ya tsere daga hannun beli kan tuhumar da ake masa na almundaha da kudade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel