Gimba: N45bn yayi kadan a gina abubuwan more rayuwa a Arewa maso Gabas

Gimba: N45bn yayi kadan a gina abubuwan more rayuwa a Arewa maso Gabas

- Majalisa tana ganin Naira Biliyan 45 sun yi wa yankin Arewa maso gabas kadan

- ‘Yan Majalisar Tarayya na so a kara kason yankin a kundin kasafin kudin 2021

- Zainab Gimba ta ce sam babu adalci a kason da gwamnatin shugaba Buhari tayi

A ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020, ‘yan majalisar wakilan tarayya su kayi tir da kason da aka gutsura wa yankin Arewa maso gabas a kasafin kudi.

‘Yan majalisar suna ganin Naira biliyan 45.32 da gwamnatin tarayya ta ware domin yi wa daukacin yankin abubuwan more rayuwa a 2021, sun yi kadan.

Jaridar Vanguard ta ce har ila yau, ‘yan majalisar suna ganin kason hukumar NEDC mai kula da cigaban yankin na Arewa maso gabas ba zai iya wani tasiri ba.

KU KARANTA: Zulum ya hadu da Sojojin Kamaru

Honarabul Zainab Gimba mai wakiltar yankin Borno ta gabatar da korafi yayin da ta mike a zauren majalisar a ranar Talata, tana neman a gyara kasafin kudin.

Zainab Gimba tace tattalin arzikin yankinsu ya shiga halin ha’ula’i a sakamakon rikicin Boko Haram, don haka ake bukatar a narka kudi a wannan shiyya.

Gimba tace ta’adin Boko Haram sun hada da rusa hanyoyi, makarantu da jawo karancin abinci.

A karshe, majalisar wakilan ta amince da cewa shugabannin kwamitocin kudi, kasafi da na NEDC su zauna da gwamnatin tarayya domin a kara kason yankin.

KU KARANTA: Gwamna Borno, Babagana Umar Zulum ya jagoranci taron NEGF

Gimba: N45bn yayi kadan a gina abubuwan more rayuwa a Arewa maso Gabas
Shugaban kasa a Majalisa
Asali: Twitter

Hon. Gimba ta kuma tado batun kudin da aka ware saboda annobar COVID-19, ta ce kason yankinta Arewa maso gabas ya yi kadan, ba ayi masu adalci ba.

A kwanaki kun ji cewa kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas a karkashin Babagana Umar Zulum ta yi taro a Jihar Adamawa domin shawo kan matsalolinta.

Abin da majalisar tarayyar ta yi shi ne matsayar gwamnonin Arewa maso gabas, wanda a taron na su, sun bukaci ‘yan majalisa su ki na’am da kasafin kudin 2021.

NEGF ta ce abin da aka ware domin abubuwan more rayuwa a kaf yankin bai zarce 0.35% daga cikin kasafin kudin Naira tiriliyan 13..02 da da aka amince da shi ba.

Jihohin na Arewa maso gabas sun koka kan rashin damawa dasu a gwamnatin tarayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel