Shehu Sani yace toshe iyakokin kasar nan da aka yi bai amfanar da komai ba
-Shehu Sani ya soki rufe iyakoki da aka yi na tsawon wata-da-watanni
-Tsohon ‘Dan majalisar yana ganin ba muci ribar komai da matakin ba
-Sani yace noman shinkafa ya damu gwamnatin tarayya ba wani abu ba
Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi magana game da rufe iyakokin Najeriya da aka yi, ya ce hakan bai taimaka wa kasar da komai ba.
Shehu Sani ya rubuta a Twitter cewa: “Rufe iyakokinmu da mu kayi bai yi wani tasiri wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga da kuma ta’addanci ba.”
Sani ya ce: “Bal ma, sai dai ya ta’azzara wahala da masifa a kan mutanen da ke kan iyakoki.”
KU KARANTA: A soke rajistar da aka yi wa Jam’iyyar APC – PDP ga INEC
A cewar tsohon ‘dan majalisar, yunkurin hana shigo da shinkafa ya sa gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasa ba komai ba, kuma ba a ci riba ba.
“Illa-iyaka, maganar shinkafa ce kawai, bai wuce nan, kuma har yanzu bamu cikin wadanda suka fi kowa noma ko fitar da shinkafa waje.” Inji Sani.
Shi kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da gwamnoni cewa ya garkame iyakokin kasar ne domin dakile shigowar makami da kwayoyi.
Ya ce: A zama na da gwamnonin jihohi yau (jiya), na yi bayanin cewa an rufe iyakokin kasa ne domin ayi maganin fasa kaurin makamai da kwayoyi.”
KU KARANTA: Ana zargin Gwamnan Imo da yi wa Jam’iyyar APC zagon-kasa
Mai girma Muhammadu Buhari yake cewa tun da makwabtan Najeriya sun fahimci wannan yunkuri, gwamnati za ta bude iyakokin kwanan nan.
Ra’ayin Sani ya sha ban-bam da na shugaban Najeriyar, ya ce yunkurin bunkasa noman shinkafa ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya ba maganin tsaro ba.
A jiya kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta sake taba kudin mai a Disamba, farashin lita zai ragu da kusan N5 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Ministan kwadago na kasa, Chris Ngige ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta rage farashin litar man fetur a wata yarjejeniya da NNPC.
‘Yan kasa za su ga banbamci a kudin litar mai a karo na shida daga watan Mayu zuwa yanzu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng