Ta tabbata: Ranar Lahadi za a ɗaura auren ango Isah da amarya Janine a Kano

Ta tabbata: Ranar Lahadi za a ɗaura auren ango Isah da amarya Janine a Kano

- Za a daura auren Janine Sanchez da angonta dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah a ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba

- An tattaro cewa za a kulla auren ne a babban masallacin Juma'a na Mopol Barrack da ke Panshekara

- Masoyan dai sun hadu ne a shafin zumuntar zaman ta Instagram har suka kulla soyayya a tsakaninsu

Alkawari na shirin cika tsakanin matar nan yar kasar Amurka mai shekaru 46, Janine Sanchez da masoyinta dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah mai shekaru 26.

Bisa rahoto da muka samu za a kulla aure tsakanin masoyan biyu a ranar Lahadi mai zuwa wanda yayi daidai da ranar 13 ga watan Disamba.

Za a daura auren ne a babban masallacin Juma’a na Mopol Barrack da ke Panshekara, jihar Kano, kamar yadda yake a katin gayyata na daurin auren wanda yayi fice a shafin soshiyal midiya.

Ta tabbata: Ranar Lahadi za a ɗaura auren ango Isah da amarya Janine a Kano
Ta tabbata: Ranar Lahadi za a ɗaura auren ango Isah da amarya Janine a Kano Hoto: Ibrahim Garba Tilde/BBC Hausa
Asali: Facebook

Ku tuna cewa, masu shirin zama ma’auratan sun hadu ne a shafin sadarwa ta Instagram, sannan sun ja hankalin mutane sosai a fadin Najeriya lokacin da Ms Sanchez ta yo tattaki kasar tun daga California, kasar Amurka.

KU KARANTA KUMA: Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata

Sashin Hausa na BBC ma ta wallafa batun daurin auren a Facebook inda tace: "Ango Isa Suleiman Panshekara tare da amaryarsa Janine Sanchez wadanda za a daura aurensu ranar Lahadi a Kano."

Ta zo jihar Kano don kawai ta hadu da masoyin nata da yan uwansa a watan Janairun 2020.

Idan za ku tuna, a baya Legit.ng ta rahoto cewa mahaifin saurayin ya ce zai kai wa jami'an tsaron farin kaya rahoto don neman amincewarsu.

Malam Isa wanda tsohon dan sanda ne da ya kai matakin SP, ya samu zantawa da Kano Focus a gidansa da ke Panshekara. Ya bada sharudda hudu a kan auren.

Sharadi na farko shine samun yarjewar jami'an tsaro. "Muna kokarin samun yarjewar jami'an tsaro. A matsayina na tsohon dan sanda wanda ya yi murabus, zan garzaya ofishin DSS a ranar Litinin don sanar dasu halin da ake ciki."

Sharadi na biyu shine dansa zai ci gaba da karatunsa bayan sun isa Amurka sannan sharadi na uku shine Isa zai cigaba da addininsa na Islama ko bayan sun koma can.

"Ina so yarona ya cigaba da karatu a can din kuma ya kiyaye addininsa na Islama." cewar tsohon dan sandan.

KU KARANTA KUMA: Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF

Tsohon dan sandan ya kara da cewa, "sai Jaenine Delsky ta kawo takardar yarjejeniyar tayi aure daga 'yan uwanta sannan za a a daura. Saboda addinin musulunci bai amince mace ta aurar da kanta ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel