Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata

Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata

- Yan kwanaki bayan an yi garkuwa da Alaramma Abubakar Adam a jihar Kaduna, matarsa ta haifi jarirai yan uku

- Yayinda hotunan yan ukun ya bayyana a yanar gizo, mutane na ta yi musu fatan Allah ya dawo da mahaifinsu lafiya

- Abubakar ya shiga hannun masu garkuwa da mutane a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, lokacin da yake a hanyarsa ta dawowa daga jihar Borno

Matar wani mutum mai suna Alaramma Abubakar Adam ta haifi yan uku duk maza bayan an yi garkuwa da mahaifinsu a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba.

An tattaro cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da mutumin lokacin da yake a hanyarsa ta komawa gida daga gasar karatu da ya kasance a ciki.

Al’ameen Muhammad Sameen, hadimin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, shine ya wallafa hotunan jariran a shafin Facebook.

Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata
Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata Hoto: Abubakar Adam
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kabilar Igbo ne ƙashin bayan duk wata ta'asa da ake yiwa yan Arewa a kudu, cewar ƙungiyar NEF

Ya wallafa:

“ALLAH MAI IKO, ANA WATA GA WATA!!! Alhamdulillah, yanxu nake samun labarin Matan yayana dake hannun masu garkuwa da mutane Alaramma Arc Abubakar Muhammad ta haifi 'ya'ya maza guda uku, Dukkan su maza, kuma suna cikin koshin lafiya, Muna fatan Allahu Subhanahu Wata'alah yaraya wadan nan yara Yakuma kaqarawa mahaifiyar su lafiya, Shikuma Alaramma Allah yakubutar dashi daga hannun wadan nan azzalumai. Amin. Dan Allah A cigaba da tayamu da Addu'o'i.”

Yan Najeriya da dama sun yi sharhi a kan hotunan yaran yayainda suka yi masu addu’a. Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

Aminu A. Mishawi ya ce:

“Allah ya raya su ya basu lafiya da Uwar baki ɗaya, shikuma muna rokon ALLAH s.w.a daya gaugauta kuɓutar mana dashi daga hannun waɗan nan azzalumai.”

Abdulmajid Ibrahim Elgaros ya ce:

“Allah ya rayasu yakutar dashi dakuma sauran al'umma.”

Ferlerloo T Sulerymern ya ce:

“MASHA-ALLAH Allah ya rayasu ya Kuma kubutar Dashi shikuma Alfarmar Manzan-Allah Sallallahu Alaihi Wa'Alihi Wasallam amen.”

Nas Akula ya ce:

“Ya Allah kadawo mana da malam lfy Kuma Allah ya rayamana wa annan yara Allah yai masu albarka.”

Sa'id U Abubakar ya ce:

“Allah Yarã Ya Su Chikin Rayuwa Mai Albarka,Shi Kuma Allah Yaku6utar Dashi, Alfarman Saiyidina Rasulillahi SaLLaLLãhu Alaihi Wasallam.”

KU KARANTA KUMA: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

Hudu Shehu Idris ya ce:

“Ubangiji ALLAH alfarman dangatanka annabi muhammadu (s. a. w) karaya abinda akasamu atafarkin sinnah shikuma kaku6utar dashi daga hannunsu.”

Príñçêê Sädāúkëë ta ce:

“Allah ya raya su kuma ya kubutar da mahaifinsu daga hannanu wadannan mugayen mutanan

"Ya Allah Dan sunayenka tsarkaka, ya Allah muna kamun qafa da girman manxanka Allah ka kubutar da alaramma daga hannunsu Dama dukkanin musulmi ya Allah.”

A wani labarin, 'Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace dan majalisar Jihar Taraba, Bashir Mohammed.

An sace Mohammed wanda ke wakiltar mazabar Nguroje a majalisar jihar misalin karfe 1 na daren ranar Laraba a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

The Cable ta ruwaito cewa an sace dan majalisar ne a gidansa da ke kusa da ofishin hukumar 'yan sandan farin kaya DSS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel